dailytrust

Yadda zaven gwamnoni ya zo da ba-zata

Dalilan da Gwamnan Zamfara ya sha qasa’ Gwamnonin da suka gaza kawo magadansu

Daga Isiyaku Muhammed da Daga Lubabatu I. Garba, Kano da Nasiru Bello, Sakkwato da Ahmed Mohammed, Bauchi da Amina Abdullahi, Yola

Aranar Asabar da ta gabata ce, Hukumar Zabe ta Qasa (INEC) ta gudanar da zaven gwamnoni a jihohi 28 na qasar nan, bayan xage zaven da mako xaya.

Sauran jihohi takwas da ba a gudanar da zaven ba, nasu zaven gwamnonin na gudana ne a lokuta daban-daban, saboda wasu dalilai da suka shafi hukuncin kotuna kan zaven nasu a baya.

A makon jiya Aminiya ta ruwaito jihohin da take ganin za a fi yin gumurzu a zaven, kuma hakan ya kasance inda sakamakon zaven ya zo da ba-zata a jihohin lamarin da ya bayar da mamaki.

Jihar Kano

Ga duk mai bibiyar siyasar Jihar Kano, ya san za a fafata sosai a tsakanin manyan giwayen siyasa biyu da ke jan akalar siyasar jihar wato tsohon Gwamna Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje. Wannan ya sa kowanensu ya tsaya tsayin-daka don ganin xan takararsa ne ya lashe zaven.

A zaven na ranar Asabar, xan takarar Jam’iyyar APC kuma Mataimakin Gwamnan Jihar, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna ya samu quri’u dubu 890 da 705 yayin da xan takarar Jam’iyyar NNPP, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya samu quri’a miliyan 1 da dubu 19 da 602, wanda hakan ya sa ya lashe zaven na bana.

Ana alaqanta nasarar NNPP kai tsaye da Sanata Kwankwanso da kuma aqidar Kwankwasiyya da take da ximbin masoya a jihar.

Akwai kuma masu ganin an gaji da mulkin jam’iyyar APC a jihar da qasa baki xaya, wanda hakan ya sa wasu suka zavi Abba, ba don suna Kwankwasiyya ba.

Qalubalen da ke gaban Abba

Ta vangaren matasa waxanda su ne qashin bayan zavensa kowa ya san irin gudunmawar da suka bayar a wannan lokaci wajen tsayawa tsayin-daka a zaven, kuma babbar matsalar matasa ita ce rashin aikin yi.

Matasan nan suna tunanin samun canjin rayuwa da suka samu kansu a ciki wanda kuma zai yi wuya ya iya biya musu wannan buqata nan take, lura da yanayin tattalin arziki da jihar da qasa suka samu kanta a ciki.

Haka a gefe guda akwai mutanen da suke ganin cewa zavavven Gwamnan zai iya haxuwa da katsalandan daga jagoran Jam’iyyar NNPP na Qasa, Injiniya Rabi’u Kwankwaso musamman ganin cewa Madugun kamar yadda ake kiransa ya yi takarar Shugaban Qasa bai kai bantensa ba, don haka zai iya mayar da hankalinsa ne a kan al’amuran gwamnatin Kano.

Dokta Sa’id Ahmad Dukawa malami a Sashen Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Bayero da ke Kano ya shaida wa Aminiya cewa guguwar Jam’iyyar NNPP a qarqashin jagoranta ne ya sa aka yi yayinta.

“Haka kuma ’yan Kwankwasiyya sun yi tsayuwar daka wajen tababtar da wannan gwamnati fiye da yadda suka yi a baya,” in ji shi.

A cewarsa al’ummar Jihar Kano sun gaji da gwamnatin APC lura da abubuwan da gwamnatin ta yi wa jama’a tun daga kan batun albashi da yadda aka tsattsaga filaye a birnin Kano.

Dokta Dukawa ya ce, “Idan an duba Gwamna Ganduje bai tsaya tsayin-daka wajen takarar Gawuna ba kamar yadda ya yi a zaven shekarar 2019, lokacin da yake neman zango na biyu. Za a yarda da ni irin yadda kwanaki kaxan kafin zave ya sake kaftaro wata rigimar ta qwace filaye.”

Qalubalen da ke gaban Gwaman Abba Gida-Gida

A cewar Dokta Dukawa halin da tattalin arziki ke ciki a duniya “Zai yi qoqari ya duba yadda za a farfaxo da tattalin arziki yadda za a dawo da walwala ga mutane.”

Haka kuma Dokta Dukawa ya ce wani qalubalen da ke gaban gwamnatin shi ne yadda za ta fita kunyar waxannan matasa na

Kwankwasiyya, “Idan an duba matasan nan suna da wani irin buri a kan wannan gwamnati kwatankwacin burin da muatne suka xora a kan Buhari a 2015. Matasan nan suna so su ga canji ta fuskar karatunsu da aikin yi da sana’o’insu da walwalarsu da sauransu,” in ji shi.

Ya qara da cewa, “Haka akwai qalubale ta fuskar yin mu’amala da waxanda su addini ne ya dame su, domin irinsu an sanya musu tsoron cewa ’yan Kwankwasiyya babu ruwansu da addini, don haka suna da qalubale yadda za su jawo su a jiki su nuna musu ba hakan ba ne, ta hanyar yin wasu abubuwa na addini amma fa ba wai na ci da addini ba.”

Dokta Dukawa ya qara da cewa cika alqawuran da gwamnatin ta xauka a lokacin yaqin neman zave abu ne mai wuya gare ta. “Misali abubuwa irin su masarautu da filaye waxanda kuma a yanzu an raya su kasuwanci yana gudana a cikinsu. A nan dole wannan gwamnatin ta yi taka-tsantsan wajen tava waxanan wurare yadda zai zama gyara ne ba varna ba. Idan kuma suka qi yin komai a kai shi ma qalubale ne domin wasu sun zave shi da niyyar samun wannan gyara.”

Yadda Dauda Lawal ya kayar da Gwamna Matawalle a Zamfara

A wani sakamakon zaven mai ban mamaki, Alhaji Dauda Lawal Dare xan takarar Jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara ya doke gwamna mai ci, Alhaji Bello Matawalle na Jam’iyyar APC.

A zaven, PDP ta samu quri’a dubu 377 da 726, sai APC ta zo ta biyu da quri’a dubu 311 da 976 kamar yadda Baturen Zaven, Shugaban Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi, Farfesa Qassimu Shehu ya sanar.

Idan za a iya tunawa, a zaven 2019, Kotun Qoli ce ta qwace nasarar APC, bayan da ta samu APC da gaza tsayar da xan takara ta sahihiyar hanya a zaven Jihar Zamfara, inda ta ba Gwamna Matawalle na Jam’iyyar PDP a lokacin.

Daga baya Gwamna Matawalle ya sauya sheqa zuwa APC mai mulki a matakin qasa, inda ya yi takarar neman tazarce a cikinta.

A vangare Dauda Lawal, kuwa zavensa a matsayin xan takarar PDP ya kasance mai cike da ruxani, inda kotuna a jihohin Zamfara da Sakkwato suka riqa soke takararsa, kuma bayan doguwar shari’a Kotun Xaukaka Qara da Kotun Qolin suk amince da takararsa.

Dauda Lawal ya samu nasara ne bayan karvuwar da ya samu a qanqanin lokaci, inda da yawan mutane suke da tunanin zai iya tsamo su daga matsalar rashin tsaro da tavarvarewar tattalin arziki da jihar ke fama da su.

Wani mazaunin Gusau mai suna Kabiru Zayyanu ya ce, “Mutanen Jihar Zamfara ba su tava goyon bayan Jam’iyyar PDP ba, domin suna ganin jam’iyya ce ta mayaudara da ba su da kishin talaka da qasa. A lokacin da kotu ta ba PDP nasara a 2019 tunanin mutane ya fara sauyawa ganin yanzu an samu mutane talakawa a mulki.

“Tafiya ta yi nisa shekara biyu ba abin da ya sauya a Zamfara, aka qara samun ci baya daga nan muka gane ba jam’iyya ba ce matsala, mutane ne, don haka za a gyara a samu masu son ci gaba ne kawai.

“Muna haka sai Gwamna Matawalle ya sauya sheqa zuwa APC hakan ya qara fito da tunaninmu kawai sai aka shiga laluben mutum mai damadama da zai kawo ci gaba. Dauda Lawal yana fitowa aka yi la’akari da yadda yake qoqarin taimakon jama’a sai muka yanke shawarar a gwada shi a gani,” in ji Zayyanu.

Muhammad Tsafe mai shekara 50 ya ce sun sauya Gwamna Matawalle ne domin ya kasa ciyar da jihar gaba a fannonin rayuwa da ilimi da kiyon lafiya da sauransu.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281509345434871

Media Trust Limited