dailytrust

Yadda zaven gwamnoni ya zo da ba-zata

Daga shafi na 2

Aminiya ta gano matsalar Gwamna Matawalle da iyalan Janar Ali Gusau ta taka rawa sosai wajen kawar da shi daga kujerar Gwamna, saboda tsige xansa Alhaji Mahadi Aliyu daga Mataimakin Gwamna.

Sannan ga matsalar tsaro da har yanzu ta qi ci, ta qi cinyewa, wadda ta qara fusata mutanen jihar.

Yadda APC ta qwace Sakkwato daga hannun Tambuwal

A Jihar Sakkwato kuwa, xan takarar Jam’iyyar APC, Alhaji Ahmad Aliyu ne ya samu nasara a zaven, inda ya samu quri’a dubu 453 da 661 ya doke xan takarar Jam’iyyar PDP Malam Sa’idu Umar Ubandoman Sakkwato da ratar quri’a dubu 49 da 29.

APC ta yi nasara a qananan hukumomi 18 daga cikin 23 a yayin da PDP ta samu qananan hukumomi biyar kacal.

Wasu magoya bayan Jam’iyyar PDP a jihar sun xora alhakin faxuwarsu a kan Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, wanda a cewarsu yake xaukar kowane lamari da sanyi.

Akwai kuma masu zargin an yi wani shiri ne a tsakaninsa da jagoran APC a jihar na hannun karva, hannun bayarwa, duk da sun fi bayyana cewa akwai sakaci a vangaren Gwamna Tambuwal.

A vangaren APC, sun bayyana cewa jajircewar jagoransu, da gazawar Tambuwal ne suka sa suka samu nasara a zaven.

Qalubalen da ke gaban zavavven gwamnan

Da yake bayyana manyan matsalolin da yake son magancewa, Alhaji Ahmad Aliyu ya yi alqawarin inganta fannin ilimi da harkar lafiya da kuma samar da ruwan sha.

Sauran abubuwan da ya ce zai mayar da hankali a kansu sun haxa da noma da tsaro da qarfafa matasa da inganta qananan hukumomi

Sai dai babban qalubalen da ke gabansa shi ne rashin kuxin shiga, kuma kusan dukkan alqawuran da ya xauka suna buqatar kuxi masu yawa.

Haka kuma zai tarar da ximbin bashi da ake zargin gwamnatin Tambuwal ta ciyo na biliyoyin Naira.

Haka kuma akwai matsalar tsaro da jihar ke fama da ita, musamman Gabashin Jihar Sakkwato, wanda ya daxe na fama da matsalar ’yan bindiga, inda ya yi alqawarin cewa ko kuxin Jihar Sakkwato za su qare, sai ya samar da zaman lafiya a yankin.

Sai dai masu sharhi kan al’amuran yau da kullum suna ganin akwai aiki a gabansa da idan bai tashi tsaye ba, za a iya maimaita irin lokacin Tambuwal ne, a kan matsalar rashin tsaro.

Haka kuma masana sun bayyana rashin aikin yi a

matsayin wani qalubale babba, inda a cewarsu yana taimakawa wajen ta’azzara matsalar tsaro.

Yadda Gwamnan Bauchi ya tsallake siraxin ‘taron dangi’

A Jihar Bauchi, Gwamna Bala Mohammed Abdulqadir ya tsallake siraxin ‘taron dangin’ da aka yi masa inda ya yi tazarce.

Hukumar INEC ta ce Gwamnan ya samu quri’a dubu 528 da 280 inda ya doke babban abokin takararsa Iya Mashal Saddiq Baba Abubakar na Jam’iyyar APC wanda ya samu quri’a dubu 432 da 272, sai xan takarar NNPP Sanata Halliru Dauda Jika ya samu quri’u dubu 60 da 496.

Gwamnan ya lashe qananan hukumomi 15 daga cikin 20 da suka haxa da; Alqaleri da Kirfi da Toro da Bauchi da Dambam da Zaki da Shira da Ningi da Warji da Tafawa Valewa da Dass da Vogoro da Ganjuwa da Itas Gaxau da Jamaare.

Shi kuma Mashal Saddiq Abubakar ya lashe qananan hukumomi biyar wato; Giyaxe da Katagum da Gamawa da Misau da Darazo.

Gwamnan ya fuskanci gogaggun ’yan siyasar jihar irin su tsohon Gwamnan Jihar Malam Isa Yuguda da tsohon Wazirin Bauchi Alhaji Bello Kirfi da tsohon Shugaban Majalisar Wakilai Mista Yakubu Dogara da Sanata Nazif Gamawa da Sanata Salisu Matori Xan Masanin Bauchi da Gado Da Masun Bauchi Alhaji Isa Musa Matori da Yerima Aliyu Giyaxe da tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Yahaya

Muhammad Miya da Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu da Ministan Kasuwanci Hajiya Maryam Yalwaji Katagum da Ministan Jin Qai Hajiya Sadiya Umar Faruq da sauran waxanda suka yi masa ‘taron dangi’ don kayar da shi.

Sai dai duk da wannan taron dangin, wanda kafin zaven wasu suka yi tunanin ba zai iya tsallakewa, Gwamna Bala ya tsallake siraxin.

Masu sharhi kan harkokin siyasa suna ganin Gwamnan ya samu nasara ne saboda qoqarin da ya yi wajen ganawa da masu zave da kuma ayyukan da ya yi.

Manazarta harkokin siyasa na ganin nasarar ta Gwamnan ta kawo sauyi a fagen siyasar jihar, inda a baya ake ganin duk wanda zai zama Gwamna sai Wazirin Bauchi Bello Kirfi ya goya masa baya.

Haka a mazavar Dass da Tafawa Valewa da Vogoro da ake kallon Yakubu Dogara ne madugun siyasar yankin, da duk ’yan takarar da ya tsayar suke yin nasara, a wannan karo Gwamna Bala ya lashe qananan hukumomin duk da ba ya tare da Dogara.

Wasu sun danganta faxuwar APC da matsalolin cikin-gida da suka dabaibaye jam’iyyar, inda ake tunanin jiga-jigar jam’iyyar da ba sa tare da Saddiq duk da cewa ba su fito fili sun bayyana adawarsu da shi ba.

Manyan qalubalen da suke gaban Gwamnan shi ne haxa kan ’yan siyasa, ta yadda za a saita jihar a siyasance.

Akwai qalubale matsalar biyan albashi da fansho da har yanzu ake ci gaba da fama da ita. Haka kuma akwai batun ayyukan ci gaban jihar a fannin ilimi da kiwon lafiya da kuma tsaro.

Tsugune ba ta qare ba a zaven Jihar Adamawa

A zaven Jihar Adamawa bana an fafata ne tsakanin Gwamnan Jihar Ahmadu Umaru Fintiri na PDP da Sanata A’ishatu Xahiru Binani ta APC.

An samu wani sautin murya da ya yi riqa yawo a kafafen sadarwa, inda a ciki aka ji wani yana cewa, “A taimaki matar nan.” Hakan ya sa wasu suke

zargin akwai wasu manyan ’yan siyasa daga Abuja da suke so ta samu nasarar lashe zaven.

Sai dai kuma a vangare xaya, bayyanar wannan sautin ya haifar da rashin yarda a tsakanin wakilan jam’iyyun biyu.

Ko da ’yan jarida suka tambayi jami’in Hukumar INEC da ake zargi cewa muryarsa ce aka ji, sai ya ce, “Ina nufin a taimaki mata ba matan nan nake nufi ba.” wannan amsar ta sa aka qara zargin cewa muryarsa ce.

Sai dai tsugune ba ta qare ba a zaven, inda Hukumar INEC ta bayyana zaven a matsayin wanda bai kammala ba.

Hukumar ta faxi haka ne bayan ta bayyana sakamakon zave na qananan hukumomi 21 inda Gwamna Ahmadu Fintiri ya lashe qananan hukumomi 13 da quri’a dubu 421 da 524, Sanata A’ishatu Xahiru Binani ta Jam’iyyar APC ta yi nasara a qananan hukumomi bakwai da quri’a dubu 390 da 275, wato Gwamna Fintiri ya ba ta ratar quri’a dubu 31 da 249.

Magoya bayan jam’iyyun biyu a ranar Lahadi sun gudanar da zanga-zangar lumana inda kowanne ke kira ga Hukumar INEC ta gudanar da adalci.

Hukumar ta faxi haka ne bayan ta bayyana sakamakon zave na qananan hukumomi 21 inda Gwamna Ahmadu Fintiri ya lashe qananan hukumomi 13 da quri’a dubu 421 da 524, Sanata A’ishatu Xahiru Binani ta Jam’iyyar APC ta yi nasara a qananan hukumomi bakwai da quri’a dubu 390 da 275, wato Gwamna Fintiri ya ba ta ratar quri’a dubu 31 da 249.

Sababbin gwamnoni

Kawo yanzu Jam’iyyar APC ta samu nasarar lashe zave a jihohi 15, yayin da PDP ta lashe 6, sai NNPP ta lashe Jihar Kano.

Sababbin gwamnonin APC

1. Ahmad Aliyu - Sakkwato

2. Bassey Otu - Kuros Riba

3. Dikko Umar Raxxa - Katsina

4. Francis Nwifuru - Ebonyi

Ci gaba a shafi na 4

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281522230336759

Media Trust Limited