dailytrust

Yadda zaven gwamnoni ya zo da ba-zata

Daga shafi na 3

5. Hyacinth Alia - Benuwai

6. Uba Sani - Kaduna

7. Umaru Bago - Neja

8. Umar Namadi - Jigawa

Sabon Gwamna daga NNPP 1. Abba Kabir Yusuf - Kano Sababbin gwamnonin PDP

1. Caleb Mutfwang- Filato

2. Dauda Lawal Dare - Zamfara

3. Kefas Agbu - Taraba

4. Sheriff Oborevwori - Delta

5. Siminialayi Fubara- Ribas.

6. Umo Eno - Akwa Ibom. suka

Gwamnonin da tsallake rijiya da baya Babajide Sanwo-Olu

A yayin zaven wasu gwamnoni sun samu yintazarce da suka haxa da Gwamnan Jihar Legas, Babajide SanwoOlu wanda ya samu quri’a dubu 762 da 134, ya kada ’yan takarar LP, Gbadebo Rhodes-Vivour da PDP Dokta Olajide Adediran.

Zaven na Legas ya yi zafi bayan Jam’iyyar Labour ta doke APC a jihar a zaven Shugaban Qasa.

Inuwa Yahaya

A Jihar Gombe, Gwamna Inuwa Yanaya ya sake lashe zavensa karo na biyu domin yin tazarce, bayan gwagwarmaya, inda a zaven Shugaban Qasa PDP ta bayar da mamaki.

Sai dai Gwamna Inuwa ya samu nasara, inda ake zargn wataqila an samu sulhu ne a tsakanin vangarensa da na Sanata Xanjuma Goje.

AbdulRazaq

Shi ma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya lashe zavensa karo na biyu domin tazarce a mulkin jihar a qarqashin Jam’iyyar APC duk da an sa ran zai fuskanci turjiya daga tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, wanda ke jan ragamar siyasar mahaifinsa da take da tasiri a jihar.

Mai Mala

A Jihar Yobe, Gwamna Mai Mala Buni ne ya samu nasarar tazarce bayan ya doke xan takarar PDP da NNPP. Gwamnan ya tsallake rijiya da baya ne, ganin yadda a zaven Shugaban Qasa PDP ta lashe jihar, lamarin da ya sa jikin magoya bayan APC ya yi sanyi.

Seyi Makinde

Gwamna Seyi Makinde na Jam’iyyar PDP shi ma ya lashe zavensa duk da cewa an yi tunanin zai samu matsala saboda rikicin cikin gida da jam’iyyar ke fama da shi da kuma yadda Jam’iyyar APC ta lashe jihar a zaven Shugaban Qasa. Gwamna yana cikin gwamnonin PDP biyar da suke adawa da takarar Atiku Abubakar. Nasarar Tinubu ta sa an riqa tsoron ya rasa kujerarsa a zaven.

Dapo Abiodun

A Jihar Ogun, Gwamna Dapo Abiodun ne ya yi tazarce a qarqashin Jam’iyyar APC da

Mai Mala Buni

quri’a dubu 276 da 298, inda ya doke Ladi Adebutu na Jam’iyyar PDP wanda ya samu quri’a 262,383. An yi ta fargabar rikicin da ke addabar APC a jihar ya kawo masa cikas.

A.A Sule

Gwamna Abdullahi Sule nan Jihar Nasarawa ya samu tazarce, bayan lashe zavensa karo biyu. Gwamnan ya fuskanci barazanar jam’iyyun PDP da LP da SDP, ganin yadda suka taka rawa a zaven Shugaban Qasa.

Bala Mohammed

Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ma ya yi tazarce bayan ya sha gwagwarmaya musamman ganin yadda aka yi masa taron dangi domin kayar da shi.

Matasan da suka lashe zaven majalisu

Rasheed xan marigayi Sanata Buruji Kashamu, ya lashe zaven Majalisar Jihar Ogun don wakiltar mazavar Ijebu ta Arewa 1, inda ya kayar da Sylvester Niyi Abiodun, na Jam’iyyar APC da ke kan kujerar. Rasheed ya lashe zaven ne yana da shekara 26.

A Jihar Kwara, Ruqayyat Shittu mai shekara 26 ta lashe zaven Majalisar Jihar don wakiltar mazavar Owode/ Onire a Qaramar Hukumar Asa ta jihar.

Rukayyat ta lashe zaven ne da quri’a 7,521 a qarqashin Jam’iyyar APC, inda ta doke xan takarar PDP, Abdullah Magaji wanda ya samu quri’a 6,957.

Rukayyat ta fara siyasarta ce daga jami’a, inda ta kasance Shugabar Qungiyar Xaliban Jami’ar NOUN.

A Jihar Nasarawa, Muhammad Adamu Oyanki, wanda ya yi takara a Jam’iyyar PDP ya lashe zaven Majalisar Jihar domin wakiltar mazavar Doma ta Arewa.

Oyanki ya samu quri’a 11,677, inda mai biye masa na Jam’iyyar APC mai mulki a jihar ya samu quri’a 9,520.

A Jihar Yobe, wani matashi mai shekara 35 mai suna Musa Lawan ya kayar da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Ahmad Lawan Mirwa, da ke neman tazarce.

Rahotonni sun ce matashin wanda xan PDP ne, wannan ne karo na biyu da suka fafata da Ahmad Mirwa, wanda ya shafe shekara 20 a majalisar.

Jami’in tattara sakamakon zaven Mazavar Nguru, Dokta Habib Muhammad ya ce matashin ya ci zaven ne da quri’u, 6,648, yayin da Shugaban Majalisar ya samu quri’a 6,466, wato tazarar quri’a 182 a tsakaninsu.

Ana ganin haka a matsayin nasara ce ga matasan Najeriya, musamman ganin yadda aka daxe ana kiraye-kirayen sanya matasa a harkokin siyasa.

A watan Mayun shekarar 2018 ne Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan dokar not-tooyoung-to-run, wadda ta ba matasa dama shiga a dama da su a harkokin siyasar qasar nan.

Sai dai a lokacin wasu sun riqa cewa a siyasar Najeriya kuxi sun fi shekaru muhimmanci.

A dokar, an rage shekarun takara, inda aka mayar da shekarar yin takarar majalisar jiha da Majalisar Wakilai daga shekara 30 zuwa shekara 25, Majalisar Dattawa da Gwamna daga shekara 35 zuwa 30, yayin da aka mayar da na Shugaban Qasa daga shekara 40 zuwa 30, sannan aka bayar da dama ga wanda yake so ya tsaya ba tare da jam’iyya ba.

A siyasar bana, an yi rajistar masu kaxa quri’a miliyan 93 da dubu 469 da 8, kamar yadda Hukumar INEC ta sanar, inda a ciki, kashi 39.65 , wato quri’a miliyan 37 da dubu 60 da 399 ke hannun matasa masu shekara tsakanin 18 zuwa 34.

Siyasar addini da qabilanci sun taka rawa a zaven 2023

Wani abu da ya xauki hankalin mutane a siyasar bana shi ne yadda addini da qabilanci suka yi kaka-gida a ciki.

Jam’iyyar Labour ta yi tashe a siyasar bana, amma an fi yi mata kallon jam’iyyar mabiya addinin Kirista.

Haka kuma takarar Musulmi da Musulmi na Shugaban Qasa da APC ta yi a qasa da Jihar Kaduna ya qara zafafa siyasar addini. Hakan ya sa an qara samun rabuwar kai, inda yanzu haka ake zaman tankiya a jihohin Legas da Kaduna kuma kai ya qara rarrabuwa.

Da yake bayani a game da hakan, Dokta Sa’id Ahmad Dukawa ya ce siyasar addini da qabilanci sun yi tasiri ne a zaven 2023 sakamakon abin da APC ta yi na tsayar da Musulmi da Musulmi a takarar Shugaban Qasa.

“Wannan abu da Jam’iyyar APC ta yi shi ya ja hankalin Kiristoci ya tashi suka mayar da lamarin na addini. Da a ce ba a yi zave ya zo ya shige lafiya ba, to da wannan abin zai yi ta bibiyar qasar nan a yi ta fargabar varkewar rigima. Ko kuma a ce da Musulmin ba su samu nasara ba, to nan gaba idan wani yana so ya haxa masu addini iri xaya a matsayin shugaba da mataimaki sai abin ya zama matsala. A yanzu yana nuni da cewa gobe ma za a iya maimaita takarar Musulmi da Musulmi ko Kirista da Kirista. Ma’ana dai duk wanda ya cancanci tsayawa takara zai iya yin abinsa ba tare da samun wata matsala ba. To da a ce Jam’iyyar APC ta sauya ra’ayinta to da wata rana ko da muqami ba za a ba wani ba saboda addininsa.

“Haka shi ma batun qabilanci ’yan qabilar Ibo su ne suka fito da wannan qarara suka nuna cewa idan ba xan qabilarsu ba, to ba wanda za su zava amma sai dai ba ta kai musu ba. Kuma daga haka za su koyi darasi su san cewa wannan hanyar da suka bi ba mai vullewa ba ce. Haka shi ma xaukar vangaranci yadda ’yan Arewa suka xauki Atiku suka nuna cewa ai xan Arewa ne don haka ba za a yarda ya faxi ba. To shi ma yanzu an gane cewa nan gaba ba za a sake yin irin wannan siyasar ba,” in ji shi.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281535115238647

Media Trust Limited