dailytrust

Yadda addini ya yi tasiri a zaven Gwamnan Jihar Taraba

Daga Magaji Isa Hunquyi, Jalingo

Wata takarda da ake zargin ta fito daga Qungiyar Kiristoci ta Qasa (CAN) reshen Jihar Taraba ana gab da zaven Gwamnan Jihar, inda a ciki ta umarci Kiristocin jihar su zavi xan takarar PDP, Agbu Kefas kuma kada su zavi wanda ba Kirista ba, ta tayar da qura, sannan ta qara rura wutar bambancin addini a jihar.

Sai dai kuma kasancewar ba xan takarar PDP ba ne kaxai Kirista, sai sauran suka nuna rashin jin daxinsu game da haka.

’Yan takarar su ne Sanata Emmanuel Bwacha na Jam’iyyar APC da Xanladi Baido na Jam’iyyar SDP sai Sanata Joel Xanlami lkenya na Jam’iyyar LP.

’Yan takarar uku sun kira wani taron manema labarai a Jalingo kafin zaven, inda suka nuna rashin jin daxinsu kan yadda qungiyar ta cusa maganar addini a harkar siyasar.

Bincike ya nuna cewa, addini ya yi tasiri a zaven na bana matuqa, musamman bayan fitar wancan takarda, inda a lokutan baya, Qungiyar Kiristocin takan yi irin hakan ne a asirce. Abubuwa biyu da suka ja akalar zaven Gwamna a jihar su ne kuxi da addini.

Sai dai Aminiya ta lura akwai Musulmin da suka zavi Kiristoci kuma wasu Kiristocin sun zavi xan takara Musulmi.

Sakamakon zaven wanda aka samu matsaloli da hayaniya da rikice-rikice a wasu wurare, xan takarar PDP, Agbu Kefas ne ya lashe shi.

Farfesa Ahmed Mohammed Abdulazeez wanda ya bayyana sakamakon zaven, ya ce Agbu Kefas na Jam’iyyar PDP ya samu quri’a dubu 257 da 926, sai xan takarar NNPP, Farfesa Sani Muhammed Yahaya ya samu quri’a dubu 202 da 272 shi kuma Sanata Emmanuel Bwacha ya samu quri’a dubu 142 da 562.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281548000140535

Media Trust Limited