dailytrust

Makomar Gwamnonin G5

Daga Isiyaku Muhammed

Tun bayan zaven fidda-gwani na takarar Shugaban Qasa na Jam’iyyar PDP, da Alhaji Atiku Abubakar ya doke Gwamnan Jihar Ribas, Mista Nyesom Wike aka fara samun rikici a jam’iyyar.

Rikici ya qara zafi ne lokacin da Atiku ya zavi Gwamnan Jihar Delta, Mista Ifeanyi Okowa ya mara masa baya, maimakon Wike, wanda ya ce Atiku da PDP sun yi masa alqawari.

Aminiya ta ruwaito yadda Jam’iyyar PDP ta shirya zaven gwaji domin zaven wanda zai mara wa Atiku, inda Wike ya zo na xaya.

Wannan ya sa Wike da wasu gwamnoni biyar suka ware, suka fara yaqi da takarar Atiku.

Gwamnonin na G5 sun gindaya wasu sharuxxa da dole a cika musu kafin su yi sulhu, su mara wa Atiku baya, daga ciki har da buqatar Shugaban Jam’iyyar PDP na Qasa, Iyorchia Ayu ya sauka.

Hakan ya qi samuwa har lokacin zaven Shugaban Qasa da aka yi ba tare da goyon bayan gwamnonin ba.

Gwamnonin su ne Nyesom Wike na Jihar Ribas da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu da Okezie Ikpeazu na Abiya da Samuel Ortom na Binuwai da kuma Seyi Makinde na Oyo.

Aminiya ta gano cewa, Atiku Abubakar ya faxi a jihohin gwamnonin biyar a zaven Shugaban Qasa.

Xan takarar Labour, Peter Obi ne ya lashe zave a jihohin Enugu da Abiya, inda Bola Tinubu ya lashe sauran uku, wato Oyo da Binuwai da Ribas.

Daga cikin gwamnonin biyar, Ortom da Ikpeazu da Ugwuanyi da Wike duk sun kammala wa’adinsu na biyu, sai Makinde ne kawai ya nemi tazarce.

Yaya makomar gwamnonin

da qoqarinsu a zaven? Ikpeazu

Gwamnan Abiya, Okezie Ikpeazu ya yi takarar sanata ne, sannan ya tsayar da Okey Ahiwe domin takarar Gwamnan da zai maye gurbinsa.

Gwamna Ikpeazu ya sha kaye a takarar Sanatan Abiya ta Kudu, inda xan takarar Jam’iyyar APGA, Enyinnaya Abaribe ya doke shi. Gwamnan ya samu quri’a dubu 28 da 422, shi kuma Abaribe ya samu quri’a dubu 49 da 693.

Haka kuma xan takararsa na

Gwamna, Okey Ahiwe ya da faxi inda xan takarar LP, Alex Otti ya samu nasara a kansa.

A lokacin haxa wannan rahoto ba a kammala haxa sakamakon ba, amma Otti yana da quri’a dubu 172 da 246 shi kuma Mista Ahiwe na PDP na da quri’a dubu 78 da 628.

A Abiya ta Tsakiya, Jam’iyyar Labour ce ta samu nasara a zaven sanata, inda xan takararta, Darlington Nwokocha ya doke xan takarar PDP, Kanar Austin Akobundu (mai ritaya), sannan a Abiya ta Arewa Sanata Orji Kalu na APC ya lashe.

Wike

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike bai yi takarar komai ba, amma xan takararsa na Gwamna, Sim Fubara ya yi nasara a PDP, inda ya samu quri’a dubu 302 da 614, xan takarar APC, Tonye Cole ya samu quri’a dubu 95 da 274.

Haka ’yan takarar sanata da ya tsayar, ciki har da mataimakiyarsa ne suka lashe zaven sanatoci uku na jihar.

Wannan ya sa Wike yake cewa, “Zaven ya nuna kowa a fili. Na kawo Gwamna da sanatoci uku da ’yan Majalisar Wakilai mafi yawa da dukkan ’yan majalisar jiha. Ayu bai kawo komai ba. Shi ma Babangida Aliyu bai kawo komai. Don haka waye ya ci amana? Muna nan a PDP. Wannan ya sa muka ce a yi abin da ya dace suka qi.”

Ugwuanyi

Shi ma Ugwuanyi ya sha qasa a takarar sanata da ya yi a Enugu ta Arewa, inda xan takarar LP, Okechukwu Ezea ya doke shi.

Okechukwu Ezea ya samu quri’a dubu 104 da 948, shi kuma Ugwuanyi ya samu quri’a dubu 46 da 948.

A zaven Gwamnan Jihar, xan takarar PDP, Peter Mbah ne ke kan gaba da tazara kaxan, inda xan takarar LP, Chijioke Edeoga ke biye masa a shekaranjiya Laraba da muke haxa wannan rahoto.

Ortom

Shi ma Gwamna Ortom ya yi takarar Sanatan Binuwai ta Kudu, inda ya sha kaye a hannun xan takarar APC, Titus Zam.

Titus Zam ya samu quri’a dubu 143 da 151, Ortom ya samu dubu 106 da 882.

Haka a zaven Gwamna, xan takarar APC, Rabaran Hyacinth Alia ya lashe zaven da quri’a dubu 473 da 933 xan takarar PDP, Titus Uba ya samu quri’a dubu 223 da 913.

Makinde

A cikinsu, Makinde na Jihar Oyo ne kaxai ya sake tsayawa takarar Gwamna, wanda a lokacin ake tunanin ya yi kuskure. Sai dai zaven ya zo masa da sauqi, inda ya samu quri’a dubu 563 da 756 ya kayar da xan takarar APC, Teslim Folarin wanda ya samu quri’a dubu 256 da 685.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281556590075127

Media Trust Limited