dailytrust

Sojoji sun kashe hatsabibin xan ta’addar nan Nagona

Sojin Najeriya sun hallaka Umaru Nagona, xaya daga cikin jagororin ’yan ta’adda da suka addabi yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Umaru Nagona, wanda a lokacin rayuwarsa ya addabi qauyukan qananan hukumomin Isa da Sabon Birni da ke Gabashin Jihar Sakkwato ya gamu da ajalinsa ne bayan sojoji sun ritsa shi, shi da yaransa.

Da yake tabbatar da labarin, Basharu Altine Guyawa Isa, wanda masani ne a kan matsalar ’yan bindiga a Gabashin Sakkwato ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, “Xan bindiga

Umaru Nagona! Yanzu dai tabbas yana Lahira. Shi ne ya ci zarafin mutanen qasar Isa da xaukacin Gabashin Sakkwato. Har yanzu akwai sauran ’yan uwansa riqe da makamai suna ci gaba da cin zarafin mutanen yankin musamman Isa da Sabon Birni.”

Game da yadda ya gamu da ajalinsa, masani a kan rikicin ’yan bindigar, Malam Abdul’aziz Abdul’aziz ma ya ce, “Yanzu nake samun tabbacin kisan babban xan bindiga, Ummaru Nagona a wata arangama da sojojin Najeriya a ranar Laraba (ta makon jiya) da ta gabata. Motar atilare ta soja ce ta take shi a kan babur da yake kai tare da yaron da ya goyo a hanyarsu ta zuwa kai agaji sakamakon harin da sojojin suka kai a sansanin ’yan bindiga a yankin Kagara ta Gabashin Shinkafi. Ummaru Nagona ya fitini Gabashin Sakkwato, musamman qauyukan da ke qananan hukumomin Isa da Sabon Birni.”

Abdul’aziz ya qara da cewa, ya haxu da Ummaru Nagona a ziyarar da ya kai w Bello Turji a watan Disamban shekarar 2021, inda ya ce, “Idan ka gan shi ba za ka ce xan bindiga ba ne. Mugu bai da kama.”

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281565180009719

Media Trust Limited