dailytrust

Rashin tsaftataccen ruwan sha na barazana ga yara miliyan 78 a Najeriya

Daga Ishaq Isma’il Musa

Asusun Yara na Majalisar Xinkin Duniya (UNICEF) ya ce, kimanin yara miliyan 78 suna fuskantar haxarin kamuwa da cuttutukan da suke yaxuwa ta ruwan sha.

Wannan bayyani yana qunshe ne a cikin wata sanarwa xauke da sa hannun Babbar Daraktar Shirin WASH ta Hukumar UNICEF Dokta Jane Bevan, wacce aka fitar a ranar Litinin da ta gabata.

“Kaso xaya cikin uku na yara a Najeriya ba sa samun tsaftattacen ruwan sha a gidajensu, kana kaso biyu cikin uku na yara ba su da makewayi. Ba kasafai ake mai da hankali wajen kula da tsaftar hannu ba, inda kaso uku cikin huxu na yara qanana ba su da halin wanke hannayensu sakamakon rashin tsaftattacen ruwa da kuma sabulu a gidajensu,” in ji ta.

Wannan dalili ne ya sa Najeriya kasancewa xaya daga cikin qasashe goma da suke fama da mutuwar yara sakamakon cuttutukan da ake kamuwa da su dalilin rashin wanke hannu kamar cututukan da suka danganci amai da gudawa.

Ta yi kiran a bai wa batun samar da tsaftattacen ruwan sha da zai dace da muhalli da lafiyar jiki kula. Ta ce, xaukar wannan mataki ba kare lafiyar yaran kawai zai yi ba, amma zai taimaka wajen tabbatar da xorewar al’umma mai zuwa nan gaba.

Ta ce, “Na tabbata muna buqatar inganta kular da muke bayarwa a wannan fanni ba tare da vata lokaci ba, har da samun kuxaxe daga Asusun Muhalli na Duniya da inganta hanyoyin kare muhalli a Shirin WASH da al’ummomin da ake gudanar da shirin.”

Ta qara da cewa “A inganta tasiri da hanyoyin bin diddigi da qwarewa domin samar da ruwan mai tsafta, sannan a qaddamar da qudirin Majalisar Xinkin Duniya na SDG6 tare da la’akari da shirin inganta tsarin.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281573769944311

Media Trust Limited