dailytrust

’Yan Boko Haram sun binne mayaqansu da aka kashe

Daga Sani Saleh Chinade, Damaturu

Aranar Lahadin da ta gabata ce Qungiyar ISWAP ta yi jana’izar mayaqanta da jiragen yaqin sojin sama na Najeriya ya kashe a ranar 19 ga Maris a Qaramar Hukumar Mafa, a wani qazamin hari da ya kai kan ’yan ta’addar.

Wani rahoto ya ce, jana’izar an gudanar da ita ce a ranar Lahadi a qauyukan Talwari da Muktari a Qaramar Hukumar Konduga.

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi Zagazola Makama ya bayar da rahoton yadda wasu masu xauke da makamai da ake zargin ’ya’yan Qungiyar ISWAP ne, sun haxu da ajalinsu sakamakon yunqurin afka wa garin a cikin manyan motoci da babura a qoqarinsu na kai hari kan sojoji da cibiyar tattara bayanan sirri ta Hukumar Zave ta Qasa (INEC) a garin da misalin qarfe 2 na dare, inda jiragen sojin ya yi musu dirar mikiya ya tarwatsa su.

Majiyar Aminiya ta tabbatar da cewa, cikin harin ne sojojin suka qwato manyan motoci qirar KLOX[ guda biyu da makamai da dama daga ’yan ta’addar, yayin da wasu daga cikin ’yan ta’addar suka tsere suka nufi hanyar Qaramar Hukumar Konduna da gawarwakin ’yan uwansu.

Sai dai wata majiyar ta shaida wa Zagazola cewa, ’yan ta’addar sun sha alwashin xaukar fansa kan wannan kisan da aka yi wa ’yan qungiyar tasu da ba a san adadinsu ba.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281578064911607

Media Trust Limited