dailytrust

Mata na buqatar a riqa yi musu adalci – Awosika

Daga Simon Echewofun Sunday da Bashir Yahuza Malumfashi

Shugabar Bankin First Bank, kuma mace ta farko da ta fara shugabantar bankin a Najeriya, Misis Ibukun Awosika ta ce, mata suna buqatar a riqa yi musu adalci a qasa, kasancewar su ne kaso 50 cikin 100 na al’ummar Najeriya.

Misis Ibukun Awosika ta bayyana haka ne a wani qwaryaqwaryan taro da Kamfanin CHI Limited ya shirya a Legas a makon nan, domin Bikin Ranar Mata ta Duniya.

Ta ce, adalci shi ne tantance qoqarin da kowane mutum zai iya yi domin ya samu nasara. Ta qara da cewa kasancewar mata su ne rabin al’ummar Najeriya, ya kamata a riqa ba su dama don ba da tasu gudunmawa wajen gina qasa kuma a daina raina su, domin hakan ba zai haifar wa qasar nan xa mai ido ba.

Shugabar ta buqaci matan Najeriya su fahimci inda suka gaza, su sa himma a ayyukansu domin ganin sun samu nasara a duk abin da suka sa gaba. Ta ce, kafin kowane kamfani ko ma’aikata ta ci gaba, ana buqatar kowane ma’aikaci, mace ko namiji su yi aiki tuquru. Don haka ta buqaci kowane kamfani ya samar da tsari mai kyau, ta yadda kowane ma’aikaci zai samu sauqin aiki domin samun nasara.

Daraktar Sashin Ma’aikata a Kamfanin CHI Limited, Temitope Adedayo-Ojo, cewa ta yi kamfaninsu tuni ya xauki hanyar kyautata jin daxin ma’aikata, ta hanyar samar da adalci da raba daidai a tsakanin maza da mata. A kan haka ne ma ta qaddamar da wani tsari na qarfafa wa mata gwiwa mai suna ‘Great Rubies’ a kamfaninsu.

Wasu shugabanni da suka yi jawabai domin qarfafa wa mata gwiwa a yayin taron, sun haxa da Janar Manaja ta Bankin Fidelity Bank Plc, Misis Chinwe Iloghalu da Daraktan Kasuwanci na kamfanin Chi Limited, Mista Bola Arotiowa.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281582359878903

Media Trust Limited