dailytrust

Soja ya harbe uwa da jaririnta a kan Naira 200

Rahotanni daga Jihar Neja sun cewa wani soja ya harbe wani xan acava da wata fasinja xauke da jaririnta a Unguwar Babanna da ke Qaramar Hukumar Borgu ta Jihar.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a lokacin da waxanda abin ya shafa suke dawowa gida daga kasuwar mako-mako ta Babanna.

Mazauna garin sun shaida wa Aminiya cewa, sojan ya harbi xan acavan ne saboda ya qi ba shi cin hancin Naira 200 da ya nema, harsashin kuma ya ratsa cikinsa ya samu matar tare da jaririnta.

Wani mazaunin garin, Sa’idu Babanna ya ce, “Xaya daga cikin sojojin da aka tura garin Babanna domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a ya harbe mutum uku saboda cin hancin Naira 200. A lokacin da waxanda abin ya shafa suke shiga garin Babanna da safe. Sojojin sun buqaci Naira 200 kuma a lokacin da suke dawowa daga Babanna zuwa Nigangi a Jamhuriyar Benin, sojojin sun sake neman qarin Naira 200 daga gare su, wanda suka ce ba za su iya biya ba.

“Hakan ne ya kai ga wani soja ya buxe musu wuta ya kashe mutum uku da ke kan babur xin nan take,” in ji shi.

Wani mazaunin yankin da ba a bayyana sunansa ba ya ce, “Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin.

“Waxanda abin ya shafa dai na dawowa gida ne daga kasuwa. Lokacin da suka zo da safe sai ga sojoji da yawa a kan iyakar Jamhuriyar Benin suka tare su suka karvi Naira 200 daga wajensu. Don haka a lokacin da suka dawo, sai wasu sojoji suka sake tsayar da su, suka sake neman Naira 200, nan take xan acavan ya qi bayarwa.

“Sai da suka fara ce-ce-ku-ce sai xan acavan ya buga babur xinsa da nufin tafiya, sai wani soja ya harbe shi wanda ya sa harsashin ya ratsa cikinsa, ya samu matar da yake xauke da ita, inda nan take matar da jaririnta suka mutu,” in ji shi.

Ya ce an kama sojan an kai shi Bataliya ta 221 da ke Kainji, a Qaramar Hukumar Borgu, bayan kiran da hakimi ya yi wa hukumomin soji.

Ya ce matar da jaririnta sun mutu nan take yayin da xan acavan ke karvar magani a wani asibiti a Jamhuriyar Benin.

Wata majiya ta ce, “Shiga lamarin da hakimin a yi ne ya hana lamarin rikixewa zuwa rikici a tsakanin matasa da sojoji.”

Qoqarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar

Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ci tura.

Sai dai Shugaban Qaramar Hukumar Borgu, Alhaji Suleiman Yarima, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce matar da jaririnta sun mutu amma direban babur xin ya tsira kuma yana jinya a wani asibiti da ke Parakou a Jamhuriyar Benin.

“Waxanda aka kashe sun fito ne daga Jamhuriyar Benin, waxanda suka zo kasuwa a Babanna domin yin sayayya.

Ya ce tuni aka aike da gawar mata da jaririnta zuwa Jamhuriyar Benin, amma ya ce ba zai tabbatar da ko an yi jana’izarsu ba.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281586654846199

Media Trust Limited