dailytrust

Majalisa za ta binciki yawan haxarin jirgin qasa a Najeriya

Majalisar Wakilai ta umarci kwamitinta kan harkokin sufuri ya binciki yawan haxarin jiragen qasa da ke janyo asarar rayuka da dukiyoyi a faxin qasar nan.

Hakan ya biyo bayan amincewa da qudirin da Unyime Idem (PDP, Akwa Ibom) ya gabatar wanda ya ce haxxuran jiragen qasa suna yin sanadin asarar rayuka da dukiyoyi a Najeriya.

Ya ce, “A watan Janairun 2023, an samu rahoton haxarin jirgin qasa a Kubwa da ke Abuja wanda ya yi sanadin mutuwar wata mata Selimota Suleiman, ma’aikaciyar gidan talabijin na NTA.

“A ranar Alhamis 9 ga Maris, 2023, wani jirgin qasa ya kutsa kai cikin wata motar safa ta BRT a Jihar Legas, inda ya yi sanadin mutuwar mutum shida tare da jikkata wasu da dama.

“A ranar 28 ga Maris, 2022, an kai wa jirgin qasan Abuja zuwa Kaduna hari kuma ’yan Najeriya da dama sun rasa rayukansu; yayin da wasu suka samu raunuka sannan aka sace wasu.

“Jirgin qasan Warri zuwa Itakpe ya kauce hanya a cikin dajin Kogi, inda aqalla fasinja 300 suka maqale bayan an sace fasinja kusan 20 daga tashar jirgin qasa a Igueben a Jihar Edo,” in ji shi.

Ya ce duk da halin da ake ciki na rashin kulawar da wasu ke yi, ba a tava xora alhakin faruwar hakan a kan wani ba.

Ya ce: “Waxannan al’amura marasa daxi sun faru sau da dama saboda ba a xauki matakin hana faruwarsu a gaba ba.”

Don haka majalisar ta umarci a binciki musabbabin aukuwar haxuran jiragen qasa daban-daban a faxin qasar nan.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281590949813495

Media Trust Limited