dailytrust

An kama tubabben xan Boko Haram kan kitsa kai wa sojoji hare-hare a Borno

Daga Sani Saleh Chinade, Damaturu

Sojin Bataliya ta 152 ta ‘Operation Haxin Kai’ da ke Banki a Jihar Borno, sun kama wani tubabben xan ta’addan Boko Haram, Ba’ana Badiya wanda aka fi sani da “Manci” kan kitsa kai wa sojoji hare-hare a jihar.

Wannan na zuwa ne qasa da mako guda bayan da wasu tsofaffin tsageru biyu, Goni Farouq da Amir Zabu, waxanda su ne manyan tsoffin kwamandojin Boko Haram ne suka shiga wata tattaunawa ta tarho, inda suka shirya kai haria kan sojojin.

Ba’ana yana cikin dubban ’yan Boko Haram da suka ajiye makamansu kuma al’umma ta karve su, amma duk da zubar da makamansa ya ci gaba da alaqa da abokan ta’addancinsa na baya.

Wata majiyar leqen asiri ta shaida wa Zagazola Makama, qwararre kan yaqi da tada qayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, cewa bayanan da Ba’ana ya bayar sun taimaka wa ’yan Boko Haram wajen samun nasarar yi wa sojoji kwanton vauna a lokacin da suke sintiri a Ngauri wanda ya kai ga kashe wasu sojoji a watan Fabrairun 2023.

A ranar 16 ga Maris, 2023, wanda ake zargin ya ba da wani bayani game da zirga-zirgar dakaru wanda ya bai wa ’yan ta’adda damar kai musu hari har aka kashe sojoji uku tare da jikkata wasu huxu a bayan garin Banki.

Majiyar ta ce matsalolin da wani lokaci sojoji ke samu a qoqarin kawar da ’yan ta’addar Boko Haram gaba xaya, shi ne munanan ayyukan infoma na cikin gida irin su Ba’ana.

Akwai damuwa cewa ci gaba da sakin ’yan ta’addan da suka tuba cikin al’umma ba tare da tsangwama ba na iya kawo naqasu wajen ci gaban da ake samu kawo yanzu a yaqin da ake da ’yan tawayen na Boko Haram da na ISWAP.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281595244780791

Media Trust Limited