dailytrust

Ƙarancin Naira: NLC za ta rufe dukkan ofisoshin Bankin CBN

Ƙungiyar Qwadago ta Qasa (NLC), ta umarci ma’aikata su fara zangazanga a dukkan ofisoshin Babban Bankin Najeriya daga mako mai zuwa saboda ƙarancin takardun Naira da ake fama da shi.

Shugaban Qungiyar, Mista Joe Ajaero, wanda ya yi wa manema labarai bayani a Abuja game da shirin, ya ce daga jibi

Juma’a za su fara haɗuwa sannan su fara rufe dukkan harkokin kasuwanci daga ranar Laraba mai zuwa a faɗin ƙasar nan.

A ranar 13 ga watan Maris ne Qungiyar NLC ta bai wa Gwamanatin Tarayya wa’adin kwana bakwai ta ɗauki matakan sassauta matsalar da ake fama da ita ta ƙarancin takardun Naira da kuma ƙarancin mai, ko ta kira yajin aiki na ma’aikata.

Shugaban Qungiyar ya ce, matakin zanga-zangar shi ne abu na ƙarshe da ƙungiyar za ta ɗauka, kasancewar ta bi dukkan matakan da suka kamata ta bi don ganin an samu sassauci a kan tsananin wahalar da ma’aikata da sauran al’ummar Najeriya suke sha saboda ƙarancin takardun kuɗin amma abin ya gagara.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281599539748087

Media Trust Limited