dailytrust

Ba mu gamsu da zaven Bauchi ba, za mu tafi kotu

Daga Ahmed Mohammed, Bauchi

Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi ta yi watsi da sakamakon zaven Gwamnan Jihar da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, inda Hukumar INEC ta ce Gwamna Bala Mohammed na PDP ne ya sake lashewa, bayan ya doke Iya Mashal Saddiq Abubakar (mai ritaya) na Jam’iyyar APC.

Sai dai da yake jawabi ga manema labarai a Bauchi, Iya Mashal Saddiq ya ce zaven cike yake da tashe-tashen hankali na ’yan daba da cin zarafin ’yan adawa da kuma fitar da wakilan APC daga rumfunan zave da dama a faxin jihar.

Iya Mashal Saddiq ya ce, “Kwamishinoni da shugabannin qananan hukumomin jihar, sun xauki kusan dukkan ayyukan zave musamman a garin Bauchi, inda aka ga Sakataren Gwamnatin Jihar yana ta yawo da kwamishinoni da shugabannin qananan hukumomi daga wannan cibiyar zave zuwa waccan tsawon dare, su watsa ko su fatattaki wakilan Jam’iyyar APC. A can suka karve takardun suka rubuta abin da suke so su rubuta.

“Wannan abin baqin ciki ne matuqa, baya ga tursasa ’yan Jam’iyyar APC da jami’an rumfunan zave da na tattara

Iya Marshal Saddiq Abubakar

quri’u, mun kuma samu tashe-tashen hankali a aqalla qananan hukumomi bakwai.

“Saboda haka abin da ya zo daga Warji ba shi ne haqiqanin abin da mutanen Warji suka zava ba, saboda an qirqiro alqaluma, an rubuta a takardu kuma abin da aka miqa ke nan. Abin baqin ciki ma an karvi wannan takardar,” in ji Iya Mashal Saddiq.

Ya ce, “Idan kuka zo Qaramar Hukumar Toro kuma an yi tashe-tashen hankali a yankuna da dama har an jikkata jami’in tsaron farin kaya (DSS) kuma a halin yanzu yana asibiti.

“Mun yin qoqari sosai don jawo hankalin hukumomin da abin ya shafa a kan abin da ke faruwa, amma abin takaici ba ma su duba al’amuran da suka shafi xaukar matakin da ya kamata,” in ji shi.

Sai ya yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu kuma kada su xauki doka a hannunsu, su bar jami’an jam’iyyar su tuntuvi sauran masu ruwa-da-tsaki don yanke hukunci kan mataki na gaba.

Daga qarshe ya gode wa magoya bayansa bisa haquri da juriyar da suka nuna a faxin jihar, musamman a yankunan da aka gudanar da zaven cikin kwanciyar hankali.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281608129682679

Media Trust Limited