dailytrust

Sakamakon zaven Gwamnan Katsina cike yake da magux i

— Lado Xanmarke

Xan takarar Gwamnan Jihar Katsina a babbar jam’iyyar adawa ta PDP a zaven da ya gabata, Sanata Yakubu Lado Xanmarke ya yi watsi da sakamakon zaven da Hukumar Zave ta Qasa (INEC) ta bayyana.

Ya ce, zaven na cike da maguxi da aringizon quri’u da barazana ga masu zave da ha’incin da bai tava gani a harkar zave ba.

Ya ce, “Ba mu gamsu da wannan sakamakon zave ba tun da mun san ba abin da al’umma suka zava ba ne aka bayyana.”

Xan takarar na PDP ya ce, ya kamata a daina yin zave kawai a riqa yin naxi, don yana ga hakan ya fi alheri.

Ya ce, “Zaven da ake yi yaudarar mutane ne kawai ake yi, kuma a vata musu lokaci.”

Sanata Xanmarke ya ce, ’yar manuniya ta nuna ko a lokacin yaqin neman zave, domin duk inda Jam’iyyar APC ta je kamfe ba ta ji da daxi “saboda mutane sun gaji da ita, amma mu duk inda muka je maraba ake yi da mu.”

Ya ce, “A zaven Shugaban Qasa an ga abin da ya faru, suna kan mulki amma sai da muka kada su. Idan aka lura za a ga cewa mutane a Katsina ba su fito zaven Gwamna sosai ba, saboda haushin abin da aka yi musu a lokacin zaven Shugaban Qasa, saboda abin da suka zava ba shi

aka ba su ba.”

Ya qara da cewa, “Babu kunya ba tsaron Allah aka ninka quri’u don kawai su samu nasara, wanda kuma kowa ya san cewa a zaven Gwamna mutane ba su fito sosai ba.”

Ya ce, don haka wannan sakamakon zave ba zavin jama’a ba ne, zavi ne na wasu mutane da suka zauna suka rubuta abin da suke so.

“Gaskiya za ta bayyana, domin muna wannan gwagwarmaya ce ba don kanmu ba, sai don al’ummar Jihar Katsina,” in ji shi.

Ya ce, ba za su yi wani abu da zai sava wa doka ba, za su yi abin da doka ta tanada. Don haka mutane su kwantar da hankulansu, za a yi duk abin da ya dace don qwato wa al’ummar Jihar Katsina haqqinsu.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281616719617271

Media Trust Limited