dailytrust

INEC ta yi kuskuren bayyana Abba a matsayin Gwamnan Kano — Gawuna

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma xan takarar Jam’iyyar APC a zaven da aka yi ranar Asabar da ta gabata, Dokta Nasir Yusuf Gawuna ya ce, Hukumar Zave ta Qasa (INEC) ta yi kuskure wajen bayyana Abba Kabir a matsayin wanda ya lashe zaven Gwamnan Jihar, sakamakon soke zaven wasu mazavun da aka yi.

Yayin ganawa da manema labarai, Gawuna ya ce akwatunan da aka soke sun kai a ce Hukumar Zave ta sake gudanar da zavuvvuka a wuraren kafin gabatar da kammalallen sakamako da kuma sanar da wanda ya ci.

Mataimakin Gwamnan ya ce, lura da yadda Hukumar Zaven ta bayyana zaven ’yan majalisar Jihar Kano 16 a matsayin waxanda ba su kammala ba, ya dace a ce ta xauki wannan mataki a zaven kujerar Gwamnan.

Ya ce, suna da yaqinin cewa

Allah ke ba da mulki ga wanda Ya so a lokacin da Yake so saboda haka za su bi matakan da suka dace ta fannin shari’a domin neman haqqinsu.

Mataimakin Gwamnan ya jinjina wa mutanen Jihar Kano bisa irin goyon bayan da suka ba shi, yayin da ya buqaci kwantar da hankali da kuma kauce wa xaukar doka a hannu.

Shi ma a nasa jawabi, Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai, Alhaji Alhassan Ado Doguwa ya ce, dokar zave ta yi tanadin cewa, idan aka soke zave a wasu mazavun da ka iya shafar kammalallen sakamako baki xaya, ya zama wajibi a koma domin sake gudanar da zave a waxancan wurare kafin gabatar da kammalallen sakamako.

Doguwa ya xauki lokaci yana fashin baki a kan irin kuskuren da Hukumar INEC ta yi wajen kauce wa amfani da dokokin zave.

Hukumar INEC ta bayyana Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaven Gwamnan da quri’u sama da miliyan guda.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281625309551863

Media Trust Limited