dailytrust

Buhari ya qi sa hannu kan dokar da ba majalisa damar gayyatar Shugaban Qasa

Labarai daga Abdullateef Salau da Muhammad Aminu Ahmad

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan, ya ce majalisar za ta sake nazarin dokoki 19 da majalisar ta yi wa gyaran fuska da Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ya qi sanya wa hannu.

Sanata Lawan ya bayyana haka ne a lokacin zaman majalisar na ranar Talatar da ta gabata.

Idan za a iya tunawa a cikin watan Janairun da ya gabata ne majalisar ta aike wa Shugaba Buhari dokoki 35 da ta yi wa gyaran fuska domin amincewa da su.

To sai dai a makon jiya Shugaban Qasar ya amince da dokoki 16 cikin 35 da ta aike

masa.

Sanata Lawan ya ce xaya daga cikin sababbin dokokin da Shugaban ya sa wa hannu ita ce dokar da ta tanadi samar da ’yancin kai a vangaren ba majalisun dokoki na jihohi da vangaren shari’a na jihohin kuxaxensu.

To sai dai xaya daga cikin dokokin da Shugaban qasar ya qi sa hannu a kai akwai dokar da ta bai wa Majalisar Dokoki ta Qasa da majalisun dokoki na jihohi damar gayyatar Shugaban Qasa ko Gwamna, don yin bayani kan wasu abubuwan da majalisun suke da damar aiwatarwa.

Sai kuma dokar da aka yi wa gyaran fuska wadda ta tanadi tilasta wa Shugaban Qasa ko Gwamna bin umarni ko yin biyayya ga gayyatar da majalisa ta yi masa.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281633899486455

Media Trust Limited