dailytrust

Na zaqu in sauka daga mulki — Buhari

Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ya ce ya ƙagara ya sauka daga mulkin, kamar yadda ya sha nunawa a baya cewa ya matsu ya ga ranar 29 ga Mayu domin ya miƙa mulki ga magajinsa.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a ganawar ban-kwana da jakadiyar Amurka a Najeriya mai baringado, Mary Beth Leonard, a Fadar Shugaban Qasa, da ke Abuja a ranar Talata.

Shugaba Buhari ya furta hakan ne yayin mayar da jawabi ga jakadiyar kan tambayar da ta yi masa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ma mai barin-gado ya ƙara da cewa yana son ya koma ya mayar da hankalinsa kan kula da gonakinsa da kuma dabbobinsa sama da 300 a Daura idan ya sauka daga mulki.

Shugaba Buhari, wanda ya nuna gamsuwa da irin sha’awar da ’yan Najeriya suka nuna kan dimokuraɗiyya ta hanyar zaɓen waxanda suke so a zaɓen Shugaban Qasa da na wakilan majalisun dokoki na tarayya da zaɓen gwamnoni da na na majalisun dokoki na jihohi da aka kammala, ya ce lallai dimokuraɗiyyar ƙasar nan ta bunƙasa.

Ya ce mutane sun fahimci ƙarfi da ikon da suke da shi, waɗanda idan aka ba su damar zaɓe cikin walwala da adalci ba wanda zai gaya musu abin da za su yi.

“Na yi farin ciki da yadda wasu ’yan takara suka faɗi a zaɓen,” in ji Shugaba Buhari.

Ya ce sakamakon canjin kuɗi da gwamnatinsa ta yi ba a samu kuɗin da za a ba masu zaɓe ba, wanda kuma duk da hakan ma ya ce mutane su karɓi kuɗin amma su zaɓi wanda ya kwanta musu a rai.

Shugaba Buhari ya ce ya ji daɗi yadda bai yi katsalandan a harkar zaɓen ba.

A wani labarin Amurka ta yi kira ga hukumominNajeriya su gurfanar da mutanen da suka yi wa masu zave barazana inda suka yi yunqurin hana su jefa quri’a a zaben gwamnoni da na majalisun dokoki na jihohi da aka yi ranar Asabar.

Ofishin Jakadancin Amurka ya ce an samu irin wannan matsala a Legas da Kano da wasu jihohin.

Ayarin Tarayyar Turai da ya sa ido a kan zaven ya ce Jihar Legas na daga cikin jihohin da aka samu tashin hankali da satar akwatin zave da kuma yi wa masu zave da ma’aikatan zave da masu sa-ido da ’yan jarida barazana.

Mutum 21 ayarin na EU ya ce an kashe sakamakon tashin hankalin da aka yi a lokacin zaven gwamnonin da majalisun dokokin jihohi da aka gudanar ranar Asabar.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281642489421047

Media Trust Limited