dailytrust

Shugabancin Majalisar Dattawa: Lokacina ne —Uzor Kalu

Sanata Orji Uzor Kalu

Mai tsawatarwa a Majalisar Dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin majalisar a majalisa ta 10.

Sanata Kalu, wanda ya sake lashe zaven Mazavar Abiya ta Arewa a qarqashin Jam’iyyar APC, ya bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata, yayin da yake zantawa da manema labarai a zauren majalisar da ke Abuja.

Sanata Orji Kalu ya ce lokaci ya yi da zai zama Shugaban Majalisar Dattawa kasancewarsa babban xan majalisa daga Kudu maso Gabas.

Ya ce, “Idan aka zave shi a Shugaban Majalisar Dattawa, zai zama tamkar wata gada ce ta haxa kan qasar nan.

“Na yi makaranta a Maiduguri, Jihar Borno. Na fara sana’a a Legas na yaxa ta a duk jihohin qasar nan. Sunana na farko zai zama tawagar

Najeriya, sunana na qarshe zai zama gadar haxa kan Najeriya.

Ya qara da cewar “Ku tuna, ni kaxai ne tsohon Gwamna da ban tava canza layin wayata ba sama da shekara 20 da suka gabata ba. Har yau ina amsa kiran jama’ata a duk lokacin da suka kira ni. Ba zan kashe wayoyina ba saboda ni ne Shugaban Majalisar Dattawa. Ina fata ’yan Najeriya za su yi min addu’a in zama shugaban majalisar saboda lokacina ne.”

Jam’iyyar APC mai mulki ce take da rinjaye a majalisar, inda ta samu kujera 57. Wasu daga cikin sanatocinta da ke sa ido a kan shugabancin majalisar sun fara jan hankalin takwarorinsu domin neman goyon bayansu.

Baya ga Sanata Kalu, waxanda suka fito fili suka nuna sha’awar neman muqamin, akwai Sanata Godswill Akpabio (Akwa Ibom) da Sanata Sani Musa (Neja) da Sanata Barau Jibrin (Kano) da Sanata Dave Umahi (Ebonyi).

Wasu masana na ganin cewa akwai yiwuwar Jam’iyyar APC ta miqa kujerar ga Kudu domin samun daidaiton madafun iko, musamman bayan tikitinta na Musulmi da Musulmi ya jawo cece-ku-ce, musamman mabiya addinin Kirista. Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin, ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar shugabancin majalisar.

Barau na Jam’iyyar APC, ya bayyana haka ne a ranar Laraba lokacin da yake zantawa da manema labarai a zauren majalisar da ke Abuja.

Ya ce: “Ina da niyyar zama Shugaban Majalisar Dattawa ta 10 da yardar Allah, nan da ’yan kwanaki ko makonni zan bayyana a hukumance.” Sanatan ya ce shi ya fi kowa qwarewa a cikin waxanda suke neman Shugaban Majalisar ta 10.

Ya ce ya kamata a yi la’akari da Arewa maso Yamma don zavar Shugaban Majalisar lura da wanda ya bai wa zavavven Shugaban qasa quri’a mafi yawa. Sanata Barau, ya ce bai kamata a yi dubi ga addini ba wajen zaven sabon shugaban majalisar. Ya ce, “Majalisar Dokoki vangare ne na gwamnati da zai yi la’akari da wanda zai iya aikin. “Majalisar Dokoki ta Qasa tana da damar daidaita ayyukanta a matsayin wani vangare na gwamnati, shi ya sa muke da qa’idojinmu. A bayyane yake a cikin tsarin Majalisar Dattawa cewa zaven Shugaban Majalisar zai fi dacewa da wanda ya fi gogewa.

“Daga cikin waxanda suke neman wannan muqami, ni ne na fi kowa matsayi kuma na fi qwarewa.Al’amarin dai shi ne cancanta, akwai buqatar mutum ya samu qwarewa kafin ya zama shugaban majalisar. “Ina xaya daga cikin waxanda suke burin zama shugaban majalisar ta fuskar qwarewa,” in ji shi.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281651079355639

Media Trust Limited