dailytrust

Qungiyarmu ta tashi don yaqar baqin al’adu yayin bukukuwa—FOMWAN

Daga Nasiru Bello, Sakkwato

Shugabar Haxaxxiyar Qungiyar Mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN) reshen Jihar Sakkwato Hajiya Zahra’u Maishanu ta bayyana hovvasar da suke yi wurin ganin sun tabbatar da an kawar baqin al’adu a cikin bukukuwan mata a Jihar Sakkwato.

Shugabar da aka fi sani da Amira ta ce wannan baqin al’adun haramun ne suna ci mana tuwo a qwarya a musulunci sai ka ji an kira wata ranar buki ta qauyawa ka samu ‘yar musulma da shigar nuna tsiraici bai dace ba muna ta wayar da kan mata su san abin da ya dace su yi domin gyara tarbiya kansu da iyalansu.

Hajiya Zahra’u Maishanu ta ce sai ka samu yarinya ta je irin waxan nan bukukuwan amma mahaifanta ba su sani ba don haka za mu ci gaba da faxakar da su illar lamarin domin gyara.

Da take tattaunawa da wakilinmu a Sakkwato, Malama Zahra’u Maishanu ta ce akwai bukatar mata su san hijabi ne kaxai hanyar da za ta tainake su wurin riqe mutuncinsu da tarbiyar gidansu.

Amira ta ce kowa yasan ayyukkan qungiyarsu ta wa’azi ce da karantarwa don ganin mata sun hau turba wadda ta dace da za ta taimaki tarbiyarsu da mutuncinsu.

Ta ce sukan gabatar

da wa’azin mata a lokacin watan Ramadan bayan nan suna karatun Alqur’ani a kowane qarshen wata, yanzu haka FOMWAN tana da makarantar Boko mai nazari da furamare, bayan ayyukkan taimako da muke yi ba dare ba rana.

Itama Farfesa Sa’adiya Umar Bello wadda tana cikin kwamitin amintattu na qungiya ta qasa ta tofa albarkacin bakinta, inda ta ce maganar sanya hijabi lamari ne da Allah Ya sanya wanda bai kamata yara mata da matasa suna gujewa hijabi ba, duk da muna yi fafutika a riqa sanya a hijabi a makarantun Boko.

Ta ce akwai wadda take shan wahala kan hijabi, Allah shi ne ya san dalilin sanya hijabi kowa ya san mu mata Allah Ya yi mu da daraja jikinmu ba abin wasa ba ne da zamu rinqa yin talla da shi, kuma ba don haka aka yi mu ba, ko da zinari kakai so sai ka binciki qasa kake samunsa an rufe shi, haka muke da daraja an rufe mu, sai wanda shari’a ta yarda ne kaxai zai ga jikinmu.

Ta ci gaba da cewa a cikin makarantu ana samun baragurbi da suke bijere wa karantarwar addini kuma akwai tasirin rashin tarbiya da haxuwa da baqi da suke shigo mana da al’adun da suka sava wa karantawar addini, sannan an zo ana yaxa abubuwan da suke kawar da tarbiya, wanda ya zama dole ne a tabbatar da an samu gyaran lamarin irin waxannan abubuwa, don samun sauqi da kuma yin rayuwa mai inganci bisa tsarin koyarwar Musulunci.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281659669290231

Media Trust Limited