dailytrust

Gyaran kyamara ya fi min aikin gwamnati — Jerryson

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

Wani matashi mai sana’ar gyaran kyamarar xaukar hoto a tsohuwar Kasuwar Gombe, Jerryson Tahiru ya ce ya zavi sana’ar gyaran kyamara ce a kan aikin gwamnati domin sana’a ce mai cike da rufin asiri.

Ya ce ya shekara goma yana gyaran kyamarar xaukar hoto bayan ya koya a wajen ’ya’yansa.

A cewarsa yana iya gyara kowace kyamara muddin ba ta daina aiki gaba xaya ba kuma idan ta gagare shi zai yi wuya wani ya iya gyara ta.

“Idan ka ga kyamara ba ta gyaru a wajena ba, ba wai ina alfahari ba ne, sai ka zaga wajen masu gyara da yawa ba ta gyaru ba” in ji Jerryson.

Ya ce ya koya wa yara 5 sana’ar sai da suka iya sannan suka bar ta saboda ba su xauke ta a matsayin sana’a ba, suka rungumi karatun boko saboda aikin gwamnati suke so a ransu.

Ya qara da cewa duk da ya iya sana’ar kuma ana lokacin siyasa ne yanzu, bai tava samun tallafi daga gwamnati ko daga wani xan siyasa ba, amma duk da haka sana’ar ta yi masa rana domin ya samu rufin asiri a cikinta.

Ya ce shi da yayansa Titus da ya koya masa gyaran duk sun mallaki muhalli a dalilin sana’ar kuma duk yadda rayuwa ta yi qunci suna da yadda za su yi.

“Yanzu a ce za a ba ni aikin gwamnati in bar sana’ar gyaran kyamara ba zan karva ba, domin sana’ar ta fi aikin gwamnati ’yanci,” in ji shi.

Daga nan ya ce burinsa a rayuwa ya samu kayan gyara na zamani da kuma matasan da zai koya wa sana’ar, waxanda za su riqe ta a matsayin sana’ar dogaro da kai don su tsira da mutuncinsu a rayuwa.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281668259224823

Media Trust Limited