dailytrust

‘Akwai rufin asiri a sana’ar xinki’

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Malam Mutari Tela dattijo ne da ya shafe shekaru da dama yana sana’ar xinki da irin keken nan na xorawa a kafaxa.

Ya shafe shekaru masu yawa a nan birnin Abuja, tun lokacin mulkin Babangida. Malam Mutari Tela a da yana zagawa cikin garin Abuja amma a yanzu ya koma zama a wuri xaya, inda yake ci gaba da gudanar da sana’ar tasa ta xinki. Aminiya ta ci karo da shi a lokacin da yake gudanar da sana’ar tasa a Unguwar Area 11 da ke tsakiyar Birnin Tarayya Abuja.

Malam Mutari asalinsa mutumin Jihar Katsina ne, ya bayyana cewa ya fara sayen keken xinki na sule uku kuma idan ya zo ya yi xinki, yakan sayar da keken ya samu riba ya kuma sake sayen wani.

Ya ce a gaskiya sana’ar xinki akwai rufin asiri a cikinta, domin da wannan sana’ar ya yi aure ya kuma sayi gonaki da dabbobi masu yawa, wanda har ta kai idan lokacin Sallar layya, sai dai ya kama a yanka duk a dalilin sana’ar xinki. Ya qara da cewa tun yana yawo ba ya samun komai har ta kai, a yanzu kwalliya ta biya kuxin sabulu, domin da wannan sana’ar da ake gani qarama ya taimaki mutane da dama, yana da gida, kuma yana xaukar nauyin yaransa a makaranta. “Duk da cewa ba shago ne da ni ba na zama, na xan sami wuri a nan ina ci gaba da gudanar da sana’ata,” in

ji shi.

A yanzu buqata ta Naira dubu 50 zuwa 100, in sha Allahu zan iya yin ta cikin wannan sana’ar.

Ya buqaci matasanmu da su mai da hankali wajen yin sana’a komai qanqantarta, kada su jira sai mutum yana da babban jari, domin ka ga ita wannan sana’ar na koya wa matasa da dama wanda a yanzu haka suna da shaguna na xinki a can gida da kuma Kano, kai har a nan garin Abuja.

“Lokacin da nake koyon wannan sana’ar a Kano, wata mata ce ta fara koya min ita, tun ina sa ido ina kallon yadda take yin yanka, har Allah Ya sa na qware sosai. Amma dai an xan sha wahala sosai don wata rana haka za ka fita a matsayinka na xan koyo, haka zan dawo inda nake kwana, ban sami ko kwabo ba. Haka na riqa haqura domin sana’ar ta shiga raina, kuma Allah cikin ikonsa, har na koya wa iyalaina, na kuma saya musu keken xinkin da yanzu haka suke aiki da shi. Kai lokacin da na zo nan Abuja wallahi na shigo cikin nasara, domin idan na fita yawon xinki nakan dawo da abin da ban tava tsammanin samu ba. Sai dai akwai wani qalubale da na tava fuskanta a sana’ar nan, inda wata mata ta tava ba ni kayanta in gyara amma aka yi rashin sa’a na vata mata kayan ta kuma dage sai na biya ta. To da taimakon Allah dai na samu mahaifinta ya saka baki ta yafe min. Zan kuma yi kira ga matasa da su mai da hankali wajen koyon sana’a. Lokacin jiran sai ka samu aikin gwamnati ya shige.”

A game da samun wani taimako a kan wannan sana’a gaskiya na samu tallafi sosai daga mutane waxanda suka taimake ni a dalilin wannan sana’a, kama daga Sarkin Bukuru da kuma shi maigidana da ya ba ni waje nake ci gaba da sana’ata, watau Barista Muhammad (SAN).

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281676849159415

Media Trust Limited