dailytrust

Amsoshin tambayoyi

Me ke sa haqoran wasu yara sukan yi jinkirin fitowa? Daga Iliyasu Wakili Akuyam Amsa:

Bambancin halitta ne da kuma ci-maka da yanayin inda mutum yake da sauransu. Ka san ko famfarar ma ba kowane yaro ke farawa a shekara bakwai zuwa tara ba, wasu sai sun haura shekara 10 suke farawa zuwa 13. Don haka ba matsala in dai bai kai 13 ba.

Da me macen da ta haihu ta samu qari ya kamata ta riqa tsarki? Daga A’isha Jamilu Amsa:

Da ruwan xumi mai gishiri abin da muke kira sitz bath. Idan kika qara ruwan kashe qwayoyin cuta irin su Datal ma ba matsala. Ana yi safe da yamma. Ba sai an sa sabulu ba. Ko dai ki sa gishrin (kamar cikin tafin hannu xaya) a baho ki zauna na mintuna biyar in za ki iya ko kuma ki cika babbar buta ki sa gishirin da Datal xin ki riqa yin tsarki kamar dai yadda ake wa basur.

Ni kuma tunda na haihu watana biyu ke nan ba na iya cin abinci sosai. Ko me ke kawo haka?

Daga Muhammad

Amsa: Eh, ana iya samun haka, amma an fi samun waxanda da sun haihu sai cikin ya buxe. To in dai za ki iya ki riqa yawan shan abin sha, kamar kunu. In kuma kina samu ki qara da bitamin. Abin da dai za a tambaye ki shi ne ruwan nono na zuwa sosai jariri na samu ko kuwa. Idan ba ya samu to ki tuntuvi likitarki wato ki koma asibiti.

Hafsat

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281694029028599

Media Trust Limited