dailytrust

Tsarin Cashless da hanyoyin inganta shi a Najeriya (5)

Masu ruwa-da-tsaki a tsarin Cashless Wannan tsari na Kashles dai an tsara shi ne matakimataki. Akwai ɓangarori dabandaban da kuma matsayi ko aikin da kowane ɓangare ya keɓanta da shi. Bayan Bankin CBN, akwai ɓangarori da dama da ba su danganci gwamnati ba. Waɗannan ɓangarori kowane da irin rawar da zai taka wajen tabbatar da wannan tsari. Komai na taskance ne a ƙarƙashin kulawar CBN. Masu ruwa-da-tsaki muhimmai dai sun haɗa da:

Bankin CBN

Wannan shi ne Babban Bankin Najeriya, wanda dukkan tsaretsaren hada-hadar kuɗi na banki ke ƙarƙashinsa. Matsayin babban banki wajen aiwatar da wannan tsari dai yana da yawa. Na farko, shi ne ya samar da tsarin, ta haɗin gwiwa da sauran bankunan kasuwanci. Na biyu, shi ne ya samar da dokoki da tsare-tsaren da za su gudana ƙarƙashin wannan tsari na Kashles. Na uku, shi ne ke rajistar dukkan masu ruwa-datsari a tsarin, tare da ba su lasisi don tabbatar da ingancin aikinsu, kuma tare da ladabtar da su idan sun saɓa doka. Na huɗu, shi ne samar da asalin gadar da ke haɗa bankunan kasuwanci da sauran masu ruwa-da-tsaki a tsarin, wajen aikawa da karɓar kuɗaɗe. Na biyar, bankin CBN ne ke ƙayyade tsarin mu’amala tsakanin bankuna da sauran masu ruwada-tsaki a tsarin a ɓangare ɗaya da kuma jama’ar ƙasa da ke da rajista ko aiwatar da hada-hadar kuɗi ta kafafensu.

Masu Na’urar POS

Babban Bankin Najeriya, wato CBN ya fitar da dokar da ta bai wa bankunan kasuwanci da kamfanonin hada-hadar kuɗaɗe damar aiwatar da abin da ya kira: Agent Banking ko a ce: “Tsarin Wakilcin Banki.” Wannan tsari, wanda ya samar da shi a shekarar 2015, ya bai wa bankunan kasuwanci ne damar samar da wakilai masu taimaka musu wajen aiwatar da wasu daga cikin ayyukansu. Maimakon ka je banki ko inda na’urar ATM ɗin bankinka take don cirewa ko sa kuɗi a asusunka na banki, kana iya tsayawa wajen waɗannan wakilai ka aiwatar da hada-hada ba tare da matsala ba. Waɗnnan wakilai dai dokar CBN ta kira su da sunan: Super Agents. Bayan rajista da ake musu, ana ba su na’urar POS ne, don amfani da katin ATM ɗin masu buƙata wajen cirewa ko sanya kuɗaɗe a asusunsu ko na wasunsu. Bayan bankunan da aka ba su wannan dama, ’yan kasuwa ma na iya zuwa su yi rajista don mallakar wannan na’ura ta POS. Dama galibin ƙasashen da suka ci gaba, da wannan na’ura ake aiwatar da cinikayya. Duk shagunan sayar da kayayyaki idan ka je ko asibitoci misali, za ka samu suna da wannan na’ura. Da zarar ka tashi biyan kuɗi sai kawai a karɓi katinka na ATM a sa a ciki a cire kuɗin ba tare da wata matsala ba.

Ƙarƙashin tsarin cashless, Bankin CBN ya samar da wannan tsari ne don rage yawan cinkoso a bankuna da sawwaƙe hanyoyin cinikayya da kuma bai wa mutane damar cirar kuɗaɗe cikin sauƙi. A ɗaya ɓangaren kuma, tsarin ya ba da damar samun ayyukan yi ga masu wannan sana’a. Domin akwai caji da Bankin CBN ya ƙayyade wanda masu na’urar POS ke cira a duk sa’ar da suka ba ka damar aikawa ko cire kuɗi daga taskarka ta amfani da wannan tsari. Domin su jami’an bankuna ne, ba wai sana’ar canjin kuɗi suke yi ba, saɓanin yadda wasu suka fahimta. Domin cajin da suke karɓa daga wajenka na hidimar da banki ya yi maka ne ta hanyarsu, da ta ƙunshi sauƙaƙe maka tafiyar da za ka yi zuwa banki ko inda na’urar ATM take ko ba ka damar cirar kuɗi a ranaku da lokutan da bankuna ba su buɗewa, irin su Asabar da Lahadi ko bayan ƙarfe 6 na yamma zuwa wayewar gari. A halin yanzu ana da na’urar POS guda 900,000 a Najeriya.

Samar da wannan tsarin wakilci ga bankunan kasuwanci da wasu kamfanonin hada-hadar kuɗaɗe - irin su Moniepoint da sauransu - na cikin matakan aiwatar da tsarin cashless a Najeriya.

Kamfanonin hada-hadar kuɗi ta wayar salula

Daga cikin masu ruwa-datsaki wajen tafiyar da tsarin cashless a Najeriya akwai kamfanonin hada-hadar kuɗaɗe ta wayar salula. Waɗannan su ake kira: Mobile Payment Service Providers. Daga cikinsu akwai irin su Teasy Mobile da MTN Momo wanda mallakin Kamfanin MTN ne a Najeriya. Ta amfani da waɗannan hanyoyi kana iya aikawa da karɓar kuɗi a taskarka da ka buɗe da su kaitsaye. A tsarin MTN Momo ma har basuka suna bai wa mutane. Ƙarƙashin wannan tsari na hadahadar kuɗaɗe, ana amfani da tsarin USSD ne, wato lambobin da ake shigar wa waya don aiwatar hada-hadar kuɗi kaitsaye, ba wai da manhajar wayar salula suke amfani ba. Shi ya sa, ko da ƙaramar waya kana iya yin rajista ko da a ƙauye ne kuma. Muddin akwai yanayin sadarwar wayar salula a wajen, ba matsala. Waɗannan kamfanoni suna samun lasisin hakan ne daga Bankin CBN.

Samar da wannan tsari ta amfani da kamfanonin hadahadar kuɗi ta wayar salula, wato: Mobile Payments Service Providers,

na cikin matakan aiwatar da tsarin cashless a Najeriya.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281698323995895

Media Trust Limited