dailytrust

Bankin Shige da Ficen Kayayyaki na Najeriya ya tallafa wajen tsara hanyoyi a Kogin Neja

Qoqarin Bankin Shige da Ficen Kayayyaki na Najeriya wajen bunqasa da havaka kasuwancin shiyya da shige da ficen kayayyaki ta hanyoyin ruwan Najeriya ya samu goyon baya sakamakon qaddamar da yashe gavar kogin Neja a wajen taron da Rundunar Ruwan Najeriya ta shirya a Babban Xakin Taro da ke Abuja.

Masana harkar ruwa na Rundunar Sojojin Ruwan Najeriya da Hukumar Kula da Ruwa ta Najeriya ne suka yi haxin gwiwa wajen qaddamar tsara yadda aikin zai kasance, inda Hukumar Shige da Fice ta Najeriya da Bankin Shige da Ficen Kayayyaki na Najeriya suka tallafa da kuxi domin tabbatar zirgazirga a gavar kogin Neja da nufin bunqasa kasuwanci.

Daina amfani da Tashar Burutu a tsakiyar shekarar 1970 ya haifar da daina amfani da hanyoyin ruwa wajen gudanar da kasuwanci, lamarin da ya sa ruwa ya qaru a hanyoyin tsawon shekaru, inda hakan ya haifar da matsala ga hanyoyin jiragen ruwa.

Idan za a iya tunawa cewa, a ‘yan shekarun baya Hukumar Shige da Ficen Kayayyaki ta Najeriya ta fara aikin samar da hanyar jirgin ruwa ta shiyya, wanda zai shafi kasuwancin shiyya ta hanyar rage lokacin da ake vatawa wajen tafiyetafiye da kuma kuxi da nufin bunqasa kasuwanci.

An qara faxaxa aikin, inda ya haxa

da samar da hanyoyin ruwa da nufin inganta zirgazirgar manyan jiragen ruwa musamman wajen xebo ma’adanai.

Shugaban Bankin NEXIM, Mr Abba Bello ya ce, ‘‘Bankin Hukumar Shige da Ficen Kayayyaki ta Najeriya kasancewarsa na bankin kasuwanci ya fara yunqurin wajen samar da kayan aiki a ruwa domin rage kashe kuxi da nufin bunqasa kasuwanci ta hanyar Aikin Shiyya na Sealink

‘‘A matsayinsa na jagora musamman a

qarqashin haxin gwiwar gwamnati na ‘yan kasuwa, manufar Sealink ita ce taimaka wa bankin wajen bunqasa shigo da kayayyaki’’.

A saqonsa na fatan alheri, Shugaban Bankin Afreximbank, Prof. Benedict Oramah wanda ya samu wakilcin Manajan Shiyya Mr. Remigius Nwachukwu ya yaba da qoqarin Hukumar NEXIM da Rundunar Sojojin Ruwan Najeriya da kuma Hukumar Kula da Gavovin Ruwa ta Najeriya wajen tallafa wa kasuwancin shiyya a Afirka sannan ya jadda shirin Bankin Afreximbank na tallafa masu saka hannun jari domin samun alfanun damarmakin kasuwanci a vangaren ruwa.

Ministan Kuxi da Kasafi Shamsuna Ahmed wadda ta samu wakilcin Mohammed Ali, Draktan Harkokin Kuxi na Gida ya bayyana cewa, ma’aikatar ta xauki aikin a matsayin xaya daga cikin nauye-nauyen da aka xora mata saboda buqatar da ke akwai wajen tallafa wa shirin wanda ‘‘zai inganta da kuma jawo hankalin ‘yan kasuwa domin saka hannun jari a vangaren sufurin ruwa.

A jawabinsa, Shugaban Sojojin Ruwa, Riyal Adimiral A.Z Gambo ya gode wa dukkanin masu ruwa da tsaki sannan kuma ya tabbatar da alqawarin Rundunar Ruwan Najeriya wajen samar da tallafin da ake buqata domin kammaluwar aikin na Kamfanin Sealink.

Ya jaddada irin rawar da Rundunar Sojojin Ruwan Najeriya suka taka wajen tantance aikin, wanda masana ruwa na rundunar suka yi, inda ya qara da cewa, wannan shi ne karon farko da rundunar ta samar da abu na gida

Ministan Sufuri, Alhaji Jaji Sambo wanda ya zamto babban baqo mai jawabi a wajen taron ya tabbatar da qudirin Ma’aiktar Sufurin na cim ma nasarar manufar shirin.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281706913930487

Media Trust Limited