dailytrust

Yadda Hanyoyin Biyan Kuxi ta Intanet Suke Bunqasa Sakamakon Gyare-gyaren Bankin CBN

A‘yan shekarun da suka gabata, Babban Bankin Najeriya ya fara gyare-gayare ka’in da na’in. musamman ta fuskar fasahar sadarwa, lamarin da ya sake fasalin hanyoyin biyan kuxi a Najeriya.

A yunqurinsa na inganta harkokin kuxi, Bankin CBN ya yi qoqarin samar da kyakkyawan yanayi domin qirqirar hanyoyin biyan kuxi ta intanet waxanda suka maye gurbin hanyoyin biyan kuxi na gargajiya musamman ta fuskar tura kuxi.

Hanyoyin biyan kuxi ta intanet na qara bunqasa, wanda ya yi sanadiyar samar harkokin tattalin arziki, duba da cewa adadin ‘yan Najeriya fi miliyon 206.

Hukumar Sadarwa ta Najeriya ta bayyana cewa, kaso 82% na ‘yan Najeriya suna da wayar hannu sannan waxanada suke siyan datar intanet sun kai miliyon 153 a Oktoban 2022, wanda hakan ke nuna cewa Najeriya ta kai ta fara gudanar da harkokin tattalin arziki ta intanet.

Idan za a iya tunawa, a 2021 Kamfanin NIBSS da Babban Bankin Najeriya da Bankuna Kasuwanci na Najeriya sun yi haxin gwiwa wajen qaddamar da fasahar NQR, wadda hanya ce ta biyan kuxi ta hanyar amfani da kod domin taimaka wa harkokin kuxi a qasar nan.

Wannan fasaha ta kod ta gida ce wadda Kamfanin NIBSS ya qirqire ta domin maye gurbin hanyar biyan kuxi kamar na’urar PoS. Sai dai ita wannan hanya ba ta kai kashe kuxin irin na na’urar PoS ba, amma tana buqatar wayar iska a wannan lokaci na annoba.

Haka kuma, wannan fasaha ba ta buqatar haxa na’ura da kati wajen biyan ko cire kuxin ta hanayar xaukar hoto.

A yayin qaddamar da fasahar, Mataimakiyar Gwamnan Bankin CBN a Vangaren Harkokin Kuxi, Aishah Ahmad ta bayyana cewa shigo da fasahar ta dace, inda ta ce za ta ci gaba da xora hanyoyin biyan kuxi na Najeriya a kan tsarin biyan kuxi na duniya.

Ta ce, ‘‘Tsarin biyan kuxi ta Najeriya ya wanzu kimanin shekara goma da ta gabata, bayan ci gaban fasaha wadda ta samu sakamakon qa’idoji waxanda suka haifar da ci gaban qirqire-qirqire a vangaren harkokin kuxi.

‘‘Tabbas, Najeriya ta wuce qasashen da suka ci gaba da dama a vanagaren fasahar harkokin kuxi’’.

‘‘Annobar Kwarona ta qara samar wa kamfanonin hada-hadar kuxi wajen qirqirar fasahohin harkokin kuxi da kuma hanyoyin biyan kuxi. Duniya ta sauya zuwa fasahar amfani da iskar waya, inda qasashe da dama kamar Cana da Tailan da Maleshiya da indiya da Singafo da Ghana da Najeriya keg abagaba wajen samar da wannan fasaha’’.

Ta qara da cewa, ‘‘ Sakamakon wannan ci gaba da aka samu, a watan Junairu Bankin CBN ya samar da wannan fasaha ta amfani da kod wajen biyan kuxi a Najeriya a matsayin wani yunquri na qara qarfafa amfani da intanet wajen biyan kuxi a qasar nan.

Wannan fasaha za ta tabbatar da gamsasshiyar hanya ga masu amfani da tsarin kod a Najeriya da sauaransu.

‘‘ Samuwar fasahar biyan kuxi ta NQR jim kaxan bayan bayyanar fasahar amafani da kod za ta cike givin hanyoyin biyan kuxi da ta wanzu a Najeriya.

Fasahar za ta game tsarin amfani da kod a faxin qasar nan, inda za ta bayar da damar biyan nan take ta hanyar gamsar da abokan hulxa daga darajar kasuwanci ta p2b da B2B’’.

Sakamakon sa-toka-sa-katsi da ake game da halarcin ci gaba da amfani da tsohuwar takardar kuxi ta 500 da 1000, ‘yan Najeriya sun rungumi hanyoyin intanet wajen gudanar da harkokinsu na kuxi.

Saboda haka, alqaluman da Kamfanin NIBSS ya bayar ya nuna cewa, ‘yan Najeriya sun rungumi amfani da hanyar biyan kuxi ta intanet, inda harkokin kasuwancin da aka qulla ta wannan hanya a shekara 5 ta kai Naira biliyon 5.2 a 2022 daga Naira miliyon 729.2 a 2018 wanda yake nuna qaruwa da kaso 613.1%.

Qaruwar harkokin kasuwanci ta intanet ya nuna samuwar qirqire-qirqire a hanyoyin biyan kuxin Najeriya.

Shi ma kuxin intanet na Bankin CBN wato eNaira wanda guda ne a cikin hanyoyin biyan kuxi ta intanet ya samu shahara ta fuskar yawan qulla kasuwanci da shi da kuma daraja musamman a wannan lokaci na aka sake fasalin takardun Naira da kuma taqaita adadin kuxin da za a cira daga asusu.

eNaira na qara samun karvuwa sakamakon amfanin da hukumomin gwamnati da makarantun ilimi da vangaren sufuri suke da shi.

Karvuwarsa ta kai cibiyar kasuwanci wato Kano, inda qungiyar masu adaidaita sahu saka karve shi hannu biyu a mtsayin hanyar biyan kuxi.

Ana iya ganin hoton kod na eNaira varo-varo a bayan adaidaita sahu a garin Kano.

A wata hira da aka yi da mai adaidaita sahu mai suna Aminu ya ce, eNaira ta kawo qarshen matsalar bayar da canji a yayin da fasinjoji suka bayar da manayan takardun kuxi.

An tsara kod xin eNaira ne domin domin masu adaidaita sahu riqa karvar Naira 100 a kan mafi yawan wurare, inda fasinjoji za su xauki hoton kod xin domin biyan kuxin zuwa eNaira wallet xin mai adaidaita sahun.

Aminu ya qara da cewa, masu adaidaita sahun da ba su da manyan wayoyi suna amfani da eNaira ta hanyar USSD wato *997# wajen biyan kuxi cikin gaggawa.

Ya ce, babbar garavasar da ke tattare da eNaira shi ne rashin caji a kan kowane kasuwanci da aka qulla da eNaira ga tabbaci da kuma sauqin shigowar kuxi da kuma ajiyewa.

Alqaluman Nigeria Inter-Bank Settlement System (NIBSS) sun nuna cewa, an samu qaruwar yawan tura kuxi ta intanet da kaso 142% wanda kuxinsu ya kai tiriliyon 19.4 a 2022 savanin tiriliyon 8 a 2021.

Hakazalika, akwai yuwuwar ci gaba da qaruwar yawan amfani da hanyoyin intanet wajen qulla kasuwanci, musamman idan aka yi la’akari da dokar taqaita cire kuxi ta Naira 500,000 ga xaixaikun mutane da 1,000,000 ga kamfanoni wadda ta fara aiki a ranar 9 watan Junairu, 2023.

Masu sharhi sun yi imanin cewa, duba da ci gaba da wayar da kai da ake game da alfanun eNaira, kamar rashin caji da ragin kaso 50% na cajin ‘yan kasuwa, ‘yan Najeriya da dama za su rungumi eNaira a matsayin zavinsu wajen gamsar da buqatunsu na yau da kullum.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281715503865079

Media Trust Limited