dailytrust

Ba a ci zarafina ba — A’ishatu Humaira

Fitacciyar jarumar Masana’antar Kannywood, wadda ta hannun damar mawaqi Dauda Kahutu Rarara ce, A’ishatu Humaira ta ce, tana cikin qoshin lafiya babu wanda ya ci zarafinta.

Jarumar ta bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafinta na

Instagram, inda a ciki ta ce an xan samu hayaniya lokacin da ta je kaxa quri’a, amma daga baya ta koma.

Aminiya ta ruwaito yadda a ranar zave jarumar ta je zave, wajen ya kaure da hayaniya, duk da cewa ba a san ainihin abin da ya faru ba.

Sai dai a ranar ta wallafa a shafinta na Instagram cewa, “Na je filin zave tun da safe, amma suka tayar da hayaniya suka hana ni yin zave. Da na ga abin yana neman zama rigima, sai na koma gida. Cikin ikon Allah na sake komawa tare da goyon wasu mutane da yawa da suka taimaka min na samu na kaxa quri’a. Sun qi, amma Allah Ya so, alhamdulillahi. Ina godiya ga dukkan waxanda suka taimaka min.”

A bidiyon da ta saka daga baya, ta ce ta yi ne domin ta kwantar da hankalin masoyanta da ’yan uwa da abokan arziki da suka kalli bidiyon lokacin zuwanta wajen zaven, inda a ciki ta qara da cewa tana cikin kwanciyar hankali kuma lafiyarta qalau babu abin da ya shafe ta.

Idan ba a manta ba, A’isha Humaira ce kan gaba wajen qurar da ta tashi a masana’antar kwanaki kafin zave, kan batun ’yan asalin Kano da baqi, inda ita da maigidanta ake yi musu kallon baqi a Jihar Kano, amma suke gaba-gaba a siyasar Kano.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281719798832375

Media Trust Limited