dailytrust

Zaven bana na neman qara ‘wargaza’ Kannywood

Dauda Kahutu Rarara Daga Isiyaku Muhammed

Aranar Litinin da gabata ce aka sanar da Abba Kabir Yusuf, wanda xan Kwankwasiyya ne a matsayin wanda ya lashe zaven Gwamnan Jihar Kano, inda ya kayar da Dokta Yusuf Gawuna na APC.

Aminiya ta sha ba da labarin yadda Masana’antar Kannywood ta rabu uku a siyasance, wato tsagin YBN da 13×13 waxanda dukkansu ’yan APC ne da kuma tsagin Kwankwasiyya.

Sai dai rikicin cikin-gida ya yi qamari a tsakanin YBN, qarqashin jagorancin Abdul Amart da 13×13 qarqashin jagorancin Dauda Kahutu Rarara, waxanda a da abokai ne.

Rikicinsu ya qara zafi lokacin da Rarara ya xauki Sha’aban Sharaxa a Kano, ita kuma YBN ta tsaya a APC a sama da qasa.

Daga baya Rarara ya dawo tallata Gawuna, inda nan ma aka yi zargin an watsar da tsagin Abdul Amart, waxanda suka daxe suna tare da Gawunan.

’Yan Kannywood sun daxe suna cewa sun shiga siyasa ce don su samu damar gogayya da masu riqe da madafun iko da nufin kawo ci gaba a masana’antar.

Sai dai Aminiya ta lura maimakon samun ci gaba, siyasar tana ta qara raba kan masana’antar da qara fito da varaka.

’Yan tsagin Kwankwasiyya, sun daxe suna zargin cewa ana musu bi-ta-da-qullin siyasa a Kano, inda nan ne cibiyar fim xin Hausa.

Aminiya ta ruwaito yadda aka kama tare da tsare Darakta Sanusi Oscar 442 bisa zargin sa da karya dokokin fim na jihar.

A lokacin kamun na Oscar, Masana’antar Kannywood ta xauki zafi, inda wasu fitattun jarumai da suke tare da Kwankwasiyya a lokacin irin su Misbahu Ahmed da Abba Almustapha da Sani Danja da sauransu suka fito suka soki Hukumar Tace FinaFinai ta Jihar Kano a qarqashin Isma’ila Na’abba Afakalla, sannan suka yi kira da a gaggauta sakin Oscar xin.

Wannan ya sa nasarar Abba Kabir Yusuf ta tayar da qura, inda wasu suke tunanin za a samu sulhu da maslaha domin ciyar da masana’antar gaba.

Sai dai ana cikin haka ne Alhaji Mustapha Sheshe wanda xan Kwankwasiyya ne ya wallafa bidiyon waqar Rarara, wadda ya yi ana gobe zave, inda a cikin ya yi gugar zana ga Kwankwanso (da yake kira tsula) cewa ya faxi zave, sannan ya ce Gawuna ya kayar da

Abba.

A qasan bidiyon, Alhaji Sheshe ya rubuta cewa, “Tsuttsula mata bulala.”

A wani rubutun daban, Sheshe ya ce, “Yanzu waye a qasa? Wanda ya yarda da Allah ko kuma wanda ya yarda da aikin boka? Boka ya karvi kuxin ’yan fansho ya karve kuxinsu. Allah Ya tsine wa uwar bokanya ma ba boka ba.” Sannan ya qara da cewa, “xan Kahutiya mara daraja xan marasa daraja.”

Daga baya ya ce, “Ku yi haquri da wasu rubuce-rubuce da na yi da mabiyana ba su saba ganin ina yi ba. Na yi ne saboda wasu dalilai ba don haka xabi’ata take ba. Ni xan Adam ne wanda dole ina da zuciyar da ake iya fusata ta. Na rama rashin girmamawa ne ga wanda ya yi rashin girmamawa ga wanda na fi qauna a siyasar Najeriya, don haka ku yi min afuwa.”

A nasa vangaren, Darakta Sanusi Oscar 442 ya sanya wani bidiyo wanda a ciki zavavven Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam yake cewa shi Oscar xin ya sha tabara ya sha maganin mayu, sai ya rubuta a qasa cewa, “Ku yi haquri maqiyan jiharmu ’yan Kannwood. Wallahi babu wanda za mu cutar a cikinku. Kuma ba mu da kamarku domin ku ne abokan sana’armu da daxi ko ba daxi. Na sha wahala sosai shekara 8 ke nan ba ni da ’yanci a cikin jihata saboda ku, babu irin sharrin da ban gani ba, na fili da na voye, haka na jure wannan rayuwa har Allah Ya yi ikonSa. Ni ba mugu ba ne, amma ku bar ni in amayar da abin da yake damu na ko na samu salama.”

A wani rubutu daban ya qara da cewa, “Ba fa za mu rama cuta da cuta ba, za mu yi qoqari mu gyara zumuncinmu da ’yan uwanmu ’yan Kannywood duk da cutar da mu da suka yi, domin biyan buqatunsu. Allah Ya sa zuwan Abba ya zama alheri ga al’ummar Jihar Kano baki xaya.”

Wannan ya sa wasu suke tunanin akwai sauran rina a kaba domin waxannan magangun sun fito ne daga wasu jagororin tsagin Kwankwasiyya waxanda suka yi baya matuqa a harkar fim na tsawon lokaci, waxanda a cewarsu an yi amfani da bambancin siyasa wajen daqile su.

Halin da jaruman masana’antar ke ciki Aminiya ta leqa shafukan sada zumunta na jaruman masana’antar don ganin yadda abubuwa ke wakana.

Ali Nuhu, wanda ya tallata Dokta Yusuf

Gawuna ya taya Abba Kabir murnar lashe zaven, sannan ya taya jaruman masana’antar ’yan tsagin Kwankwasiyya murna, inda shi kuma Alhaji Sheshe ya yi masa godiya.

Shi ma furodusa Abubakar Bashir Maishadda ya taya Abba Kabir Yusuf murnar lashe zaven da sauransu.

Sai dai Aminiya ta lura cewa, wasu jigajigan APC sun fara komawa Kwankwasiyya, duk da cewa sun daxe ba sa tare da ita.

Mustapha Naburaska, wanda hadimin Gwamna Ganduje ne ya bayyana a wata tattaunawarsa da DCL Hausa cewa dama can shi xan Kwankwasiyya ne, kuma zai koma gidansa na asali.

A cewarsa, shi bai tava aibata Kwankwaso ko Kwankwasiyya ba, kuma a shirye yake ya ajiye muqaminsa na gwamnati domin ya koma sanya jar hula.

Shi ma Madagwal, wanda a da can xan tsagin Kwankwasiyya ne, har ya fara tallata takarar Kwankwaso a zaven Shugaban Qasa na shekarar 2027.

Sai dai a wani rubutu mai kama da martani, Alhaji Sheshe ya ce, “Ku fa daina tunanin tsallaka titi, azumin nan da muka yi, sai kun yi shi, kuma ga shi naku babu ranar shan ruwa.”

Gaskiyar lamari kan harin da aka kai gidan Rarara-Baban Chinedu

A wata tattaunawa da Baban Chinedu, wanda aminin Rarara ne ya yi da kafar DW Hausa ya ce, ’yan uwansa ’yan Kannywood yake zargi da harin da aka kai musu shi da Rarara.

A cewarsa, “Dama can akwai wanda ya ce min idan suka samu gwamnati duk abubuwan da suka faru babu wanda bai ce za a yi ba. Don haka babu ruwan Kwankwaso ko Kwankwasiyya. A masana’antar akwai waxanda suna da hassada a zuciyarsu. Wannan hassada ce kawai ba wani abu ba. Akwai wani wajen adana kayayyakina da ke Hausawa, babu wanda ya san wurin sai xan fim. Yaran ba su san wurin ba, yawo da su ake yi ana nuna musu.”

Baban Chinedu ya qara da cewa ya yi asarar da ta wuce Naira miliyan 10 a harin.

Siyasar bana Kannywood za ta sha jar miya-Naziru Xan Hajiya

Da Aminiya ta tuntuvi Furodusa Naziru Xan Hajiya, wanda shi ne ya fara tsayawa takara a masana’antar a zaven bana, inda ya tsaya takarar Majalisar Jihar Kano a APC, sannan ya yi takarar Majalisar Wakilai a Jam’iyyar ADP daga baya ya ce, yana hasashen Kannywood za ta ci moriyar siyasar ta bana.

A cewarsa, “Kannywood za ta samu ci gaba sosai a yanzu fiye da baya saboda masana’antar ta tsaya tsayin-daka wajen tallata takarar zavavven Shugaban Qasa, Bola Ahmed Tinubu, kuma ya samu nasara. Wannan ya sa ba zai manta da wannan gudunmawar ba.”

Da Aminiya ta tambaye shi ko yana fargabar masana’antar za ta qara rabewa? Sai ya ce ba ya tunanin haka.

“Ai yawanci ba ma adawa da gwamnati. Yanzu haxa kai za mu yi mu mara wa gwamnati baya domin ta kai ga nasara kuma ta taimaki masana’antarmu. Mu masana’antar ce a gabanmu,” in ji shi.

A qarshe ya yi kira ga ’yan masana’antar cewa kada su bari siyasa ta shiga tsakaninsu, har su qi junansu.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281728388766967

Media Trust Limited