dailytrust

Varawo da alqali

ani varawo ne ya saci akuya, sai aka kama shi aka kai shi kotu. Ga yadda ta kwashe, tsakaninsa da alqali: Alqali: Ana tuhumar ka da satar akuyoyi uku. Varawo: Qarya ne ranka ya daxe, akuya xaya na sata. Alqali: Kada ka raina wa kotu hankali. Ga akuyoyi uku a gaban kotu a matsayin shaida. Varawo: Ranka ya daxe uwar na sata, shi ne ’ya’yanta biyu suka biyo ta. Ni kuma ba zan iya cewa su koma ba. Alqali: Kana raina kotu fa! Varawo: Ranka ya daxe, ko kai ne aka sace mahaifiyarka, ka gan ta, ai za ka bi ta. Alqali: Gaskiya ne, zan bi ta, amma ka fara zuwa kurkuku, a dawo da kai bayan wata biyu.

Daga Abba Bala Haruna Tsafe, 08167015150

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281736978701559

Media Trust Limited