dailytrust

Kinayar Bahaxeje

Wani Bahaxeje ne talauci ya kama shi, ya rasa abin da zai yi ya samu kuxi, sai dabara ta zo masa. Sai da ya bari an biya ma’aikatan gwamnati albashi a Haxeja, sai ya tafi banki, ya samu wurin na’urar ATM an cika maqil ana ta hadahadar cirar kuxi. Bahaxeje kawai sai ya baje a qasa, ya yi kamar ya suma, kumfa na fita daga bakinsa. Nan fa mutane suka yo kansa domin taimakonsa, cikinsu sai wani ya riqa cewa: “Ku samo ruwa a zuba masa domin ya farfaxo!” Jin za a kwara masa ruwa sai Bahaxeje ya maqe murya ya ce: “Ku qyale wancan wawan mai batun samo ruwa, idan da agajin ruwa nake so ai bakin Gidan Ruwa zan suma. Ba ku lura da wurin da na suma (banki) ba? Ku agaza da abin da ya dace kawai amma ba da ruwa ba!”

Daga Bashir Yahuza Malumfashi (08065576011)

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281741273668855

Media Trust Limited