dailytrust

Hali zanen dutse

ani xan sanda ne yana duba littattafan makarantar ’ya’yansa domin ganin irin qoqarinsu ko akasi, sai ya fara da babban xansa. Saboda vacin rai sai da ya yi wa yaron bulala 30. Da ya zo kan littafin qaramin sai suka ga ya kalli littafin ya fita kawai daga xakin. Bayan ya fita sai babban yake tambayar qaramin cewa: “Yaya na ga Baba bai doke ka ba, bayan na san kai ma ba ka yi qoqari ba?” Sai ya ce: “Ai Naira xari biyu na saka masa a tsakiyar littafin, shi ya sa ya qyale ni.”

Daga Abba Bala Haruna Tsafe, 08167015160

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281749863603447

Media Trust Limited