dailytrust

Yawan al’umma a Najeriya: A samar da ingantaccen tsarin kyautata rayuwa

A wannan makon, GIZAGO (08065576011) ya bibiyi yadda a kullum ake kukan yawan haihuwa kuma ake danganta matsalolin quncin rayuwa da batun na yawan al’umma. Ya bayyana mahangarsa dangane da al’amarin, inda ya samar da shawarwarin da za su magance matsalar

ANajeriya, an daxe ana ta kai kawo dangane da al’amarin yawan jama’a. Aqalla, kowace gwamnati kan yi tsare-tsare dangane da yadda za ta tafiyar da al’umma, musamman ma wajen samar da kyakkyawan yanayin tafiyar da rayuwa, wanda ya shafi tattalin arziki da ilimi da lafiya da muhaalli da tsaro da sauransu. Babbar matsalar ba ta samar da tsarin ba ce kuma ba ta yawan al’ummar da ke qaruwa a kullum ba ce. Babbar matsalar ta tsaya ne ga tafiyar da tsarin da ya dace sau da qafa.

A shekarar 2018, an ruwaito Ministar Al’amuran Kuxi ta Najeriya, Dokta Zainab Ahmed Shamsuna tana magana dangane da kawo tsarin da ya shafi taqaita haihuwa, domin samar da tsari mai kyau game da tattalin arzikin qasa. Kamar yadda ta ce a cikin harshen Ingilishi, “Mun ankara da cewa hauhawa da qaruwar jama’a ne babban qalubalenmu dangane da tafiyar da tattalin arzikin qasa. Ba mu ce Gwamnatin Tarayya za ta qayyade ‘ya’yan da mutum zai haifa ba. Gwamnati tana tuntuvar sarakunan gargajiya da malaman addini domin su ilimantar da mutanensu dangane da tazarar haihuwa, domin su riqa haihuwar adadin ‘ya’yan da za a iya kulawa da su sosai.”

Ni kuwa na ce, ba fa yawan al’umma ne ke haifar da matsin tattalin arziki ba, komai yawan al’umma, muddin aka samu tsarin gudanarwa mai kyau da shugabanci mai kyau, yawan jama’a rahama ne. Wani abin da ya kamata mu fahimta shi ne, duk wata qasa da ka ga ta ci gaba a duniya, babban abin da ya ba ta wannan shi ne yawan al’umma. A tarihin Turai, yawan al’umma ne ya yunqurar da su suka samu xaukaka a duniya ta fuskar tattalin arziki da qereqere. A tsakanin shekarar 1760 zuwa 1840, tumbatsa da yawan al’umma a Turai ne ya sanya suka maida hankali wajen qere-qere da sarrafe-sarrafe, suka bazama ko’ina a cikin duniya, musamman Afirka domin neman kasuwa da kayan sarrafawa.

A China, yawan al’umma ne ya ingiza su suka farka, suka yi nazari da karatunta-natsu,

a tsakanin shekarar 1958 zuwa 1961 suka mai da hankali kacokan kan noma da sarrafe-sarrafe da qere-qere. Sai da suka rufe qasarsu na tsawon shekaru daga shigo da wani abu na qira ko noma. Da kansu suka riqa qera duk wani abu da suke buqata, suka riqa noma duk wani abinci da suke buqata. Ta kai ga a yau China ta fi qarfin abinci da duk wani abin qereqere, sai dai ta fitar waje ta sayar kuma ita ce ta farko a duniya wajen yawan al’umma.

A Jamus, akwai lokacin da suka yi tsarin qayyade haihuwa, amma ba su ji da daxi ba, domin kuwa sai da aka samu wani lokaci, tsofaffi sun fi matasa yawa. Dole uwar na qi, dole suka sassauto. A yanzu, duk magidantan da suka samu haihuwa, har wani tallafi ake ba su, saboda yawan al’ummar suke nema.

Qasar Indiya, ita ce ta uku a yawan al’umma a duniya amma a yau tana xaya daga cikin qasashe masu tashe ta fannin tattalin arziki, qereqere da bunqasar ilimi. Me ya ba su wannan? Sun samar da tsarin gudanarwa mai kyau ga al’umma, sun sanya kishin qasa da burin ciyar da ita gaba.

Mu a nan Najeriya, ana hasashen cewa muna da adadin aqalla yawan mutane miliyan 200 ne, kuma mu ne mafi yawa a Nahiyar Afrika. Allah Ya albarkace mu da faffaxar qasar noma mai kyau. Muna da ma’adinai da sauran albarkatun qarqashin qasa masu xinbin yawa. Muna da albarkar man fetur da iskar gas. Qasar China ba ta da irin wannan albarkar, haka ma qasar Indiya, amma sun ninninka mu yawa fiye da qima. To yaya aka yi su yawan al’ummarsu bai hana su ci gaba ba? Saboda sun xauki matakin da ya dace, sun samar da tsarin tafiyar da al’umma mai kyau da dacewa, sun sanya kishin qasa da na al’umma a tafiyar da al’amuransu.

Mu kanmu a nan Najeriya, idan har za a samar da kyakkyawan tsari, za mu iya ririta yawan al’ummarmu domin mu ci gaba kuma mu bunqasa a duniya. Muna da yawan al’umma, don haka muna da kasuwa ta kai tsaye ga duk abin da muka sarrafa. Muna da wadatattar qasar noma, wacce za ta ba mu damar noma duk abin da muke buqata, har ma mu sayar wa qasashen waje. Idan har shugabanni za su daina sace-sacen dukiya suna jibgewa qasashen waje, idan har za a yi amfani da dukiyar qasa wajen samar da ingantattun makarantu da ingantattun kamfanonin sarrafa albarkatun qasa, babu shakka za mu samu nasara.

A yau a Najeriya, mutum guda sai ya sace dukiyar da mutum miliyan goma za su iya amfani da ita, daga shi sai ‘ya’yansa biyu ko uku. Sai mutum guda ya kimshe abincin mutum miliyon goma a gidansa shi kaxai. Sai mutum guda ya girke motocin alfarma guda 20 shi kaxai. Sai mutum guda ya mallaki jiragen shiga na alfarma shi kaxai. Daidai da Kansila, ‘ya’yansa na qasar waje suna karatu. Daidai da qaramin ma’aikaci a NNPC, idan matarsa ta tashi haihuwa qasar waje zai nufa. Shin ta yaya za a ci gaba?

Ko addinance ma, yawan al’umma ba shi ke gadar da talauci ko rashi ba. An samu hadisin da ke cewa, Manzon Allah (saw) ya ce, abincin mutum xaya, ya ishi mutum biyu, abincin mutum biyu, ya ishi mutum uku... Hikimar da ke cikin wannan kalamin ba ta tsaya ga abinci kaxai ba, za ta iya tasiri a dukkan al’amuranmu na rayuwa, kamar muhalli da sutura da abin hawa da sauransu.

Ya kamata gwamnatocinmu, attajiranmu, malamanmu da masananmu su yi nazari su canja tsarin gudanarwar qasar nan. A daina sata da almundahana. A hana almubazzaranci da dukiyar qasa. A maida hankali wajen samar da bunqasasshe kuma kyakkyawan tsarin ilimi. A maida hankali wajen noman zamani, wanda zai iya samar da isasshen abinci, ya samar wa xinbin matasa aikin yi. A mai da hankali wajen binciken kimiyya da qere-qere. Malaman addini su mai da hankali wajen cusa tsoron Allah ga mabiyansu da samar da haxin kai tsakanin al’umma.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281754158570743

Media Trust Limited