dailytrust

Abin tunawa lokacin aikata zunubi

Assalamu alaikum. Ina yi wa masu karatu murnar zuwan watan Ramadan mai cike da alfarma da albarkatu. Kamar kullum, ina qara tunatar da ma’aurata cewa, wannan wata naku ne, ma’aurata, wata ne na sabunta so da qauna da qara kusancin juna da kuma qara kusanci da Allah Maxaukakin Sarki. Ku tuna cewa, aure fa ibada ce, to kamar yadda dagewa wajen kyautata sauran ibadu to ibadar zamantakewar aure ma ya kamata a dage wajen kyauta ta da inganta ta don a dace da samun daxi guda biyu, ga daxin kyautata zamantakewar aure ga kuma daxin rivanya lada da ake dacewa da shi cikin wannan wata. Da fatan ma’aurata za su dage kuma kar da suyi sakaci. Ga wannan labarin da ya faru tsakanin wasu magabatan ma’aurata da fatan zai zaburar da sauran ma’aurata su dage wajen qara neman kusancin Allah Maxaukakin Sarki ta hanyar bin Umarninsa da kuma kiyaye iyakokinsa.

Abubuwan tunawa lokacin aikata zunubi

Wata kyakkyawar mace da ke zaune a garin Makkah Al-Mukarramah tana kallon fuskarta da sha’awar kyawun fuskarta a madubi, ta dubi mijinta sannan ta tambaye shi:

“Shin yanzu akwai namijin da zai ga fuskata, wanda ba zai jarabtu da ita ba?” Sai ya ce: “I, akwai shi.” Ta ce da shi: “Wane ne?” Sai ya ce: “Ubaid bin Umar.” Ta ce: “Ka amince min in gwada shi in ga ko zan iya yaudarar sa?” Maigidan nata ya amince mata.

Sai ta je wajen Ubaid Bin Umar, sai ta yi kamar tana son yi masa wata muhimmiyar tambaya mai buqatar sirri. Lokacin da ta isa wata kwana a nan masallaci mai tsarki, sai ta cire niqabinta ta bayyanar masa da fuskarta, wacce ta haskaka da kyau kamar wata xan daren goma sha huxu.

Ubaid (ra) ya tambaye ta: “Ya baiwar Allah, me kike son tambaya?” Ta amsa da cewa: “Don Allah ka cika min burina, don na samu kaina cikin kogin so da begen ka.”

Ubaid ya amsa da cewa: “Ina so in yi maki wasu ’yan tambayoyi. Idan kika amsa min su da gaskiya, zan yi qoqari game da buqatarki.”

Ta ce: “In sha Allah zan amsa da gaskiya ga dukkan yawan tambayoyin da za ka yi mini.”

Ubaid ya ce: “Idan Mala’ikan mutuwa ya zo karvar ranki, za ki ji daxin cika miki buqatarki a wannan lokacin? Sai ta ce: “Wallahi ba zan ji ba.”

Sai Ubaid ya ce: “Kin faxi gaskiya. Idan aka saka ki a cikin qabarinki, ga mala’iku za su yi maki tambaya, shin za ki ji daxin cika miki burinki a wannan lokacin?” Sai ta ce: “Wallahi ba zan ji ba.”

Sai Ubaid ya ce: “Kin faxi gaskiya. Idan za ki hau Siraxi kuma ba ki san cewa ko za ki haye ko za ki faxa ba, za ki yi farin ciki da na biya miki buqatarki a lokacin? Sai ta ce: “Wallahi ba zan ji ba.”

Sai Ubaid ya ce: “Idan aka tsai da sikeli kuma ba ki sani ba, shin ma’aunin kyawawan ayyukanki ya yi nauyi ko sakayau yake, shin za ki ji daxin da na cika buqatarki a lokacin? Sai ta ce: “Wallahi ba zan yi ba.”

Sai Ubaid ya ce: “Kin faxi gaskiya. A lokacin da kike tsaye a gaban Allah don yin lissafin ayyukanki, za ki ji daxin cewa na biya miki buqatarki a wannan lokacin? Sai ta ce: “Wallahi ba zan ji ba.”

Sai Ubaid ya ce mata: “Kin faxi gaskiya. Ya ke baiwar Allah ki ji tsoron Sa, kamar yadda ya yi maki falala mai yawa.”

Sai matar ta koma wajen mijinta, ya ce da ita: “Me ya faru?” Ta amsa da cewa: “Ashe muna ta varnatar da rayuwarmu ba mu sani ba!”

Sannan ta sadaukar da kanta wajen yin sallah da azumi da sauran ibadu. Bayan haka, mijinta ya kasance yana cewa: “Me Ubaid ya yi mini? A da kullum za ta zo min ta ci kwalliya kamar amarya amma yanzu ba ta sha’awar komai na duniya sai ibada!”

Ya Allah Ka ba mu ikon tuna waxannan al’amura duk lokacin da za mu aikata wani aiki na savon Allah, Ka kuma sa tuno su xin ya hana mu aikatawa, amin.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281767043472631

Media Trust Limited