dailytrust

Bambancin sha’awa da soyayya 6

Daga Abu-Unaisa Gabatarwa: Abu- Unaisa Darussunah Foundation, 07035888158

Ita ma vatacciyar soyayyar tana da nata tasirin wanda alamunta suna bayyana ya zama dole ga mutum ya nemi magani:a) Mutum ya gaza bayar da aikinsa kamar yadda ya dace, don zuciyarsa kullum tana wajen wata, duk xan abin da ya samu ya ba ta, in ba ta karva ba hankalinsa ya tashi, ya gaza tsayuwa a wajen aiki don yana son ya je wajen masoyi, a irin wannan matsayi dole a nemi matsaya, don ba ingantacciyar soyayya ake yi ba, sha’awa ita ce a kan gaba, da zarar an xaura aure ita matar za ta fara ganin wasu ‘yan canje-canjen da ba ta taba tsammani ba.

b) Akan samu kuma qunci da damuwa, musamman idan ya kasance mutum ya yi nesa da masoyi. Wani lokaci mutum yakan rasa abin da yake masa daxi, har da kansa ya yanke hukuncin cewa maganin hakan kawai shi ne kasancewa da masoyi, amma da a ce ingantacciyar soyayya ce, ba a yin ta inda bai dace ba, don soyayya ce da ba a rabuwa, kuma ita masoyiyar tana da damar gamsar da shi da duk abin da yake buqata, kuma a lokacin da yake so. A nan ba za a samu hauhawar sha’awa ba, sai dai son saduwa da masoyi gami da yi masa hidima.

c) Qoqarin zama da wanda ake kira masoyi ne na gaskiya kowane lokaci da son tava jikinsa in zai yuwu ko tava wuraren fitina duk dai da sunan soyayya. Mutum shi kansa ya san ya savi Allah, zuciyarsa za ta yi ta raya masa cewa Allah fa zai yi fushi da shi. Wannan in yana da xan sauran imani ke

Ka zavi babban dalilin da ya sa kake son wance, ko dalilin da zai sa ta karvi soyayyar wane, kar ya zama cewa kyawunta kawai da tsarin surarta suka fisgi hankalinsa, ko ita ta sakankace cewa zai iya biya mata buqatunta na rayuwa da zumunci don haka za ta aure shi, a yi qoqari a duba lamuran da ba sa canja wa mutum, kamar xabi’u na qwarai, son ibada, neman ilimin addini, ko shiryarwa ta qwarai.

nan a zuciyarsa. Na zauna da wani mutum da yake ce min ya kai matsayin da budurwarsa ta yi masa tayin biya masa buqata matuqar yana so. Tsoron a kama su ne kawai ya hana shi, amma duk wani nau’i na savo ya aikata, a nan zai kira sha’awar da take tsakaninsu ne da sunan soyayya, wata qila ma su ce soyayya ce ta gaskiya, alhali sam ba haka ba ne, tasirin vatacciyar soyayya ne.

d) Akwai kuma nisantar ‘yan uwa da abokai da ma kowa da kowa don dai a kaxaitu da wanda ake ganin masoyi ne, duk in ka raya wa zuciyarka cewa ba wanda zai hana ka zama da wance ko kuwa ita ta ce in sama da qasa za su haxu sai ta auri wane, ba shakka wannan tasirin makauniyar soyayya ne, wanda ake ce ma ta “hana ganin laifi”. Irin wannan ko abokai da qawaye ba su cika ba da gudummuwar a zo a gani ba wajen taimakon masoyan, domin abin da masoyiyar take so qawarta take ba ta shawara, shi ma saurayin

bai samun gamsasshiyar shawara wajen abokansa ba saboda wannan dalilin.

Domin a taimaka wa waxannan masoyan dole a bi wasu ‘yan shawarwari:a) Ka zavi babban dalilin da ya sa kake son wance ko dalilin da zai sa ta karvi soyayyar wane, kar ya zama cewa kyawunta kawai da tsarin surarta suka fisgi hankalinsa, ko ita ta sakankace cewa zai iya biya mata buqatunta na rayuwa da zumunci don haka za ta aure shi. A yi qoqari a duba lamuran da ba sa canja wa mutum, kamar xabi’u na qwarai da son ibada da neman ilimin addini ko shiryarwa ta qwarai.

b) Ya zama dole a nisanci kallon finafinan batsa da karanta littafansu. A nisanci zama da wani jinsi na dabanda son ganin wuraren da suke motsa sha’awa a jikinsa. Yanzu har hotuna na batsa da bidiyo ana iya kallo a wayoyi, su kuma sukan qara sha’awar da in mutum bai yi a hankali ba ba shakka zai faxa zuwa ga vatacciyar soyayya wace qarshenta nadama ne. Ba ina wajabta sanya niqabi ne ba wajen hira da masoyi ko hana zance gaba xaya, amma dole a guji abin da zai dauwamar da sha’awa a maimakon soyayya.

c) Kusantar Qur’ani mai girma da koyarwar Annabi (SAW) a hadisai tana matuqar taimakawa wajen rage aukawa cikin baqar soyayyar da take qarewa da nadama, masamman zama a wuraren karatun addini, inda ake gina mutum don ya fahimci aure ibada ne, neman sa kuma yana da tsari yadda addini ya wasafta, ba abu ne da mutum zai yi yadda ya ga dama ba. Duk lokacin da mutum ya samu kansa ba ya aikin komai to ya daure ya nemi abin da zai shagalta da shi, musamman ‘yan karance-karancen abubuwa masu amfani.

d) Mutum ya yi qoqari ya sa wa zuciyarsa cewa soyayya kamar dambe ce, wanda yake kallo shi yake ganin da zai naushi wuri kaza tabbas zai yi kaye, kai da kake ciki ba ka da sararin da za ka iya hango wurin. Don haka sauraron shawarwarin abokai da na gaba suna matuqar taimaka wa matashi wajen gyara rayuwar soyayyarsa, kar mutum ya ce ya fi kowa sanin abin da ya dace da shi. Raina shawarwarin uwaye alama ce babba ta makauniyar soyayya.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281775633407223

Media Trust Limited