dailytrust

’Yan APC da kansu suka kayar da Jam’iyar su a Jihar Oyo – Bashir Maiborno

Daga Kabir Yayo Ali, Ibadan

Jagoran ’yan Arewa magoya bayan Jam’iyyar APC a Jihar Oyo, Alhaji Bashir Maiborno ya yi zargin cewa magoya bayan jam’iyyar ne da kansu suka kayar da jam’iyyar a zaven Gwamnan Jihar da ya gabata.

Ya ce, “Ba Jam’iyyar PDP ce ta kayar da APC a zaven Gwamna da aka aka yi a Jihar Oyo ba, ’ya’yan Jam’iyyar APC da suka haxa da zavavvun ’yan Majalisar Dattawa 3 da wakilai 9 na Majalisar Wakilai da suka ci zave a inuwar Jam’iyyar APC a jihar su ne da kansu suka amince a kayar da APC a dalilin rikicin cikin -gida.”

Ya faxi haka ne a hira da Aminiya inda ya ce, “Sun yi haka ne a qarqashin yarjejeniyar da aka ce sun qulla da Gwamnonin PDP 5 (G5) da kuma zavavven Shugaban Qasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, cewa PDP a Jihar Oyo za ta sadaukar da ’yan takarar majalisun tarayya a zaven Shugaban Qasa a yayin da su kuma za su rama wa kura aniyarta ta fannin zaven Gwamna Seyi Makinde. Amma hakan bai yi tasiri a zaven Shugaban Qasa ba, domin duk nasarar da APC ta samu na yawan quri’u a zaven Shugaban Qasa ya biyo bayan aikin da muka yi ne da aka fake da shi wajen yin amfani da waxannan zavavvun ’yan majalisa na APC suka riqa fitowa suna yin yekuwa ga magoya bayansu su zavi Gwamna Seyi Makinde. An yi zargin sun yi amfani da kuxi wajen sayen mutane, wanda mu ba mu mallaki irin wannan kuxi ba. Amma muna godiya ga Allah da Ya bayar da mulki ga wanda Ya so.”

Shi kuwa tsohon Sakataren Jam’iyar PDP

a Jihar Oyo Alhaji Bashir Akanbi (JP) cewa ya yi, “Babban dalilin da ya sa Jam’iyyar APC ta sha kaye a zaven Gwamna a jihar, shi ne kasa tsayar da xan takarar da mafi yawan talakawa suke so. Xan takarar Gwamna da APC ta tsayar Sanata Teslim Folarin ya yi shekara 12 a Majalisar Dattawa amma babu wani abin a-zo-a-gani da ya samar wa jama’a a mazavarsa.

“Wannan ne ya sa ya fara faxuwa tun daga mazavar tasa inda jama’a suka juya masa baya. Kuma hakan ne ya ba Gwamna Seyi Makinde damar samun ximbin magoya baya musamman saboda ayyukan ci gaban rayuwa da ya shimfixa a sassan jihar a shekara 4.

“Kuma ban amince cewa yarjejeniya tsakanin Bola Ahmed Tinubu da

Gwamnoni 5 na Jam’iyar PDP ce ta kayar da APC a Jihar Oyo ba, domin kowa ya san cewa dubban mutane sun fito suna murna da farin ciki domin nuna goyon bayansu ga zaven xansu Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin sabon Shugaban Qasa. Wannan ne babban dalilin samun nasarar Tinubu a Jihar Oyo. Ka san ba za su tava juya masa baya ba,” in ji shi.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281779928374519

Media Trust Limited