dailytrust

Mahara sun qone kotu a Ebonyi

Wasu ’yan bindiga sun qone wata Babbar Kotu a yankin OwutuEdda da ke Qaramar Hukumar Afikpo ta Kudu a Jihar Ebonyi. An ce ’yan bindigar sun mamaye kotun ce a ranar Talata, inda suka qone ta tare da lalata takardun kotun.

Magatakardan Kotun, Oluchi Uduma, ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Owutu-Edda a shekaranjiya Laraba.

Ta ce ginin kotun da takardu da sauran kayayyaki masu amfani sun qone qurmus.

Shugaban Qaramar Hukumar Afikpo ta Kudu, Mista Chima Nkama, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kai rahoton lamarin ga ’yan sanda.

Lamarin na Ebonyi na zuwa ne a daidai lokacin da yankin Kudu maso Gabas ke fama da hare-hare. A watan Disamban 2022, wasu ’yan bindiga sun lalata wata Kotun Majistare da ke Owerri da kuma wata Babbar Kotu a Qaramar Hukumar Orlu ta Jihar Imo.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281788518309111

Media Trust Limited