dailytrust

’Yan bindiga sun sace budurwa sun nemi fansar miliyan 10

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wata budurwa mai shekara 19, mai suna Adetutu Okinbaloye a Unguwar Imoru da ke Qaramar Hukumar Ose a Jihar Ondo.

Aminiya ta samu labarin cewa ’yan bindigar su bakwai xauke da makamai sun kutsa cikin wani gida suka tafi da ita bayan sun raunata ’yar uwar mahaifiyarta da wuqa.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Fumilayo Odunlami-Omisanya, ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Talata a Akure.

Sai dai wata majiya a unguwar ta ce maharan sun tuntuvi iyalan budurwar inda suka buqaci a biya su kuxin fansa Naira miliyan 10.

A wani labarin makamancin haka an gano gawar wani mutum da aka ce direban motar haya ce xan garin Idanre a Akure.

Wani ganau ya ce an jefar da gawarsa ce a kusa da babbar tashar mota ta Benin a Akure.

An kuma ce wasu da ake zargin masu tsafi ne suka kashe shi inda suka yanke wasu sassan jikinsa.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281792813276407

Media Trust Limited