dailytrust

Ta babbake xanta da iyalansa

Ana zargin wata tsohuwa mai shekara 75 da banka wa xanta da jikokinta biyu da kuma surukarta wuta a Jihar Ondo.

Ana zargin tsohwar ta yi ajalin xan nata da iyalansa ne bayan ta watsa musu fetur sannan ta banka musu wuta a cikin gidansu, lamarin da ya haddasa mummunar gobara.

Aminiya ta gano cewa abin ya faru ne a wani qauye mai suna Aponmu da ke wajen garin Akure, babban birnin jihar.

Majiyarmu ta shaida mana a ranar Talatar da ta gabata aka kai magidancin da iyalan nasa Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Owo, inda likitoci suka tabbatar da cewa shi da matarsa da xaya daga cikin ’ya’yan sun rasu.

“Babban xan ne kaxai ya rayu, shi ma a yanzu haka yana cikin mawuyacin hali,” in ji majiyar.

Wakilinmu ya yi qoqarin jin ta bakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, amma hakan bai samu ba.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281797108243703

Media Trust Limited