dailytrust

An kama wanda ya yi lalata da ’yarsa a Legas

Wata Kotun Majistare da ke Ikeja a Jihar Legas, ta bayar da umarnin tsare wani mai shekara 36 a yankin Roland Okajare, a gidan gyaran hali bisa zargin lalata da ’yarsa mai shekara 18.

Alqalin kotun, E. Kubeinje, ta miqa batun ga Daraktan Shigar da Qararraki na Jihar Legas (DPP), inda ta xage sauraren qarar zuwa ranar 12 ga Afrilun bana.

Xan sanda mai shigar da qara, ASP Kehinde Ajayi, ya shaida wa kotun cewa Okajare ya aikata laifin ne a ranar 4 ga Janairu, a shagonsa da ke Tashar Mota ta Ikotun, Legas.

’Yar ta shaida wa ’yan sanda yadda ya tilasta mata ya yi lalata da ita. Ta ce ba shi ne karo na farko da mahaifin nata ke kai mata hari ba.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281801403210999

Media Trust Limited