dailytrust

Abubuwan da muke fata daga zavavvun gwamnonin Kudu —’Yan Arewa

Daga Kabir Yayo Ali, Ibadan da Daga Musa Kutama, Kalaba

Al’ummar Hausawa da sauran ’yan Arewa mazauna garuruwa daban-daban na Jihar Oyo da suka kaxa quri’unsu a zaven Gwamna da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, sun ce sun yi haka ne don nuna buqatar a tafi tare da su.

Binciken Aminiya ya gano cewa kwana uku kafin zave, ’yan takarar Gwamna a jam’iyyun PDP, Seyi Makinde da Teslim Folarin na APC da Bayo Adelabu na Accord sun ziyarci Unguwar Sabo mazaunin Hausawa a birnin Ibadan inda suka riqa shiga lungu da saqo suna ganawa da dattawa da malamai da qungiyoyi a kan a zave su.

Sai dai binciken ya gano cewa sakamakon zaven da aka bayyana a Unguwar Sabo ya nuna cewa Hausawa ba su dunqule sun zavi xan takara xaya ba, maimakon haka sun rabu gida uku wajen zaven ’yan takarar uku na PDP mai mulki a jihar da APC da Accord, inda sakamakon zaven ya nuna APC ce a kan gaba.

Bayan da Hukumar INEC ta bayyana Gwamna Seyi Makinde na PDP a matsayin wanda ya lashe zaven, Aminiya ta tuntuvi wasu daga cikin Hausawan kan irin abubuwan da suke buqata daga zavavven Gwamnan da zai yi mulkin wa’adi na biyu a jihar.

Alhaji Yahaya Dauda, jigo ne na ’yan Arewa magoya bayan Jam’iyyar PDP a Jihar Oyo, ya ce, “Muhimmin abubuwan da muke so Mai girma Gwamna Seyi Makinde ya yi mana a yanzu shi ne ya tabbatar da vullo da sabon salon siyasar kawar da qabilanci, inda ake kallonmu a matsayin baqi a wannan sashe kuma a samar da guraben karatu a manyan makarantu har zuwa jami’a ga ’ya’yanmu da xaukarsu a aikin gwamnati kamar yadda wasu jihohin Arewa suke yi wa Yarbawa.”

Shi kuwa Ustaz Tahir Zubairu cewa ya yi “Da farko zan so a ce zavavven Gwamna Seyi Makinde ya xauki kansa a matsayin uba ga dukkan al’ummar Jihar Oyo ba tare da ya qyale wasu baragurbin mutane na kusa da shi sun yi amfani da wannan dama wajen ingiza shi ga mulkin da zai raba kan al’umma ba, musamman yin amfani da addini wajen cusa gaba da qiyayya a tsakanin jama’a. Na jinjina wa Gwamna Makinde a kan bin shawarar Qungiyar Kare Haqqin Musulmi (MURIC) wadda ta nemi ya goge sunansa daga jikin bangon wani masallaci kafin ranar zave kuma ya yi hakan ba tare da vata lokaci ba. Irin haka muke buqatar gani dagga shugabanni domin samar da zama lafiya da dunqulalliyar qasa.”

Game da yadda aka gudanar da zaven, Aminiya ta ziyarci wasu wuraren taruwar al’ummar Hausawa don ji ta bakin mutane, inda suke cewa, “Ban tava ganin zaven da ya faranta min rai a Jihar Oyo kamar wannan ba, domin an gudanar da komai lami lafiya ba tare da qone-qone da kashe-kashe da aka saba yi a zavuvvukan baya ba.”

Na’urori da kayan aiki na zamani da Hukumar INEC ta yi aiki da su a rumfunan zave sun taimaka sosai wajen rage yawan dogon layin jama’a. Wannan alama ce ta ci gaba. “Babu ruwana da yadda Jam’iyyar PDP ta kayar da APC a Jihar Oyo, ni dai na san cewa ni da matata mun je mun kaxa quri’armu ga wanda muke so domin yin mulkin adalci da zama lafiya.

“Idan har da gaske ne cewa an qulla yarjejeniya a tsakanin zavavven Shugaban Qasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na APC da Gwamna Seyi Makinde na PDP a kan wannan zave, to ina ganin cewa alama ce da za ta kai Gwamna Makinde ficewa daga PDP zuwa APC a nan gaba.

“Babu wani batun siyasar addini a wannan zave da aka yi a Jihar Oyo domin dukkan mabiya addinai har da masu addiinin gargajiya da waxanda ba su da wani addini ne, suka zavi Gwamna Makinde, kuma ka san cewa kusan kowane gida ko zuriya suna cakuxe ne Musulmi da Kirista.” Muna ta yin qorafi a kan samun guraben ayyuka tun daga gwamnatocin baya da ta yanzu amma mun kasa haxa kanmu. Saboda haka idan Gwamna Makinde ya tashi cika mana alqawari zai zame mana babbar illa idan muka tafi a rabe kamar yadda ya fara aukuwa a lokacin wata ganawa da Gwamnan ya yi da mutanenmu kafin ranar zaven, inda saboda son zuciya da haxama da babakere aka kasa yin rabon adalci na abin da Gwamnan ya bayar. Wallahi za mu yi nadama muddin muka ci gaba da yin haka kuma za mu ji kunya a gaban ’ya’ya da jikokinmu a nan gaba,” in ji shi.

A ranar Talata da ta gabata Aminiya ta hango wasu qusoshin ’yan Arewa magoya bayan Jam’iyyar PDP da suka haxa da masu ba Gwamna Shawara su biyu, Alhaji Ahmed Murtala da Alhaji Hakeem Azeem da Jarman Ibadan Alhaji Xanjuma Yakubu da

Alhaji Xanladi Garba suna bi gida-gida da wuraren taruwar jama’a a Unguwar Sabo Ibadan don miqa saqon godiyar Gwamna Makinde ga ’yan Arewa da suka fito ranar zave suka kaxa masa quri’a domin ci gaba da mulkin jihar zango na biyu.

A yankin Kudu maso Gabas, Aminiya ta lura cewa har yanzu Hausawan da suka koma gida Arewa ba su fara dawo ba.

Tun zaven Shugaban Qasa Hausawa mazauna yankin suka koma Arewa saboda tsoron abin da zai iya faruwa na rikici musamman saboda bambancin siyasa.

Bincike da Aminiya ta gudanar a jihohin Delta da Ribas da Akwa Ibom ya gano cewa har yanzu wasu ’yan Arewa da suka tafi gida ba su dawo ba.

A yankin Kudu maso Gabas

ma ’yan Arewa mazauna shiyyar tsofaffin zama ne suka rage, amma sauran har yanzu ba su dawo ba, sai dai majiyoyi a yankin sun bayyana wa wakilin Aminiya cewa, “Wasu kwanan nan za a ga suna dawowa wasu kuma sai bayan azumi.

“Ko da ma wasu za su dawo ana ganin damina a Arewa gab take da faxuwa, sai sun tsaya sun yi noma ba wai tsoron tashin hankali ba ko wani abu zai faru ba,” in ji wata majiya.

Game da yadda suka jefa quri’a kuwa, Adama Shu’aibu wata matashiya ta tabbatar da cewa sun yi zave lafiya ba tare da wata hantara ba.

“Ka san a fagen zave babu nuna adawar siyasa tunda kuwa so yake ya jefa tasa ya dawo gida ya jira a faxi sakamakon zave, wasu kuma qoqari suke yi su ga sun jawo ra’ayi a zavi nasu xan takarar,” in ji ta.

A jihohin Akwa Ibom da Kuros Riba, Hausawa mazauna jihohin sun taya waxanda suka samu nasara a zavuvvukan gwamnoni da ’yan majalisa.

Ta fuskar kasuwanci kuma rashin wadatar jama’a ya sa ’yan kasuwa na kokawa da rashin ciniki saboda yawanci mutane sun tafi Arewa ba su dawo ba.

AgGarin Aba na Jihar Abiya, Sani Xahiru ya tabbatar da cewa suna nan zaune lafiya, harkokin kasuwanci na tafiya, “Domin mutanenmu ’yan Arewa mazauna jihohin Akwa Ibom da Kuros Riba na zuwa sayayyar kayan kasuwancinsu, sai dai matsalar rashin fita da Qungiyar IPOB ta kafa har yanzu babu shiga babu fita a wasu yankunan da ke Kudu maso Gabas domin duk motar da suka gani ko ta wane ne idan ta xauko kaya qona ta suke yi,” in ji shi.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281805698178295

Media Trust Limited