dailytrust

Game da zavuvvukan da aka yi

Assalamu alaikum Editan Aminiya mai albarka. Fatar alheri ga dukkan ma’aikatan jaridar. Haqiqa mu ne muke ta addu’a dare da rana, safiya da yamma a kan Allah Ya zava mana mafi alheri a cikin masu neman shugabancin qasarmu da jihohinmu da majalisun tarayya da jihohi.

Babu mai yi sai Allah, kuma don mun yi imani da haka shi ya sa muke ta roqon Allah a kan Ya zava mana mafiya alheri. Mun yarda kuma mun yi imani cewa, Allah Shi ne Mafi sanin daidai kuma shi Yake ba da mulki ga wanda Ya so, haka kuma Yana ba da Shugaba daidai da al’umma ne.

Idan Allah Ya ba ka nasara, kada ka samu damar wulaqanci ko cin mutuncin abokin adawarka na siyasa,domin siyasa qaramin lokaci gare ta, ita kuma zamantakewa tana kasancewa ne har qarshen rayuwa.

Kamar yadda idan ba ka yi nasara ba, kada ka xauka Allah ba Ya son ka ba ne. Allah Ya sa haka ne ya fi alheri domin in da rayuwa to akwai rabo a gaba.

Daga qarshe ya kamata mu taya shugabannin da aka zava da addu’a, Allah Ya yi riqo da hannayensu wajen gudanar da adalci a cikin mulkinsu. Allah Ya ba mu zaman lafiya mai xorewa a qasarmu baki xaya.

Daga Aminu Adamu Malam Madori, Jihar Jigawa,08139041679.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281814288112887

Media Trust Limited