dailytrust

Ga zavavven Shugaba Bola Tinubu

Daga Alhaji Abdulkarim Xaiyabu

Ga dukkan alamu abubuwa huxu ba su da amfani a Najeriya. (1) Arzikin Qasa (2) Mutanen Kirki (3) Ilimi

(4) hankali.

Na faxi haka ne saboda da ana yin amfani da waxannan muhimman abubuwa huxu da na jero a sama yadda ya kamata da ba mu shiga mugun halin da muke ciki a qasar nan a yanzu ba.

Daga lokacin da aka fara fitar da xanyen man fetur daga Najeriya zuwa wasu qasashe ana sayarwa zuwa ranar 1 ga Oktoban 2018 an sayar da man da ya kai na Dala tiriliyan (wato Dala biliyan 1000). Ban san yadda zan bayyana wannan adadi a Naira ba, sai dai mu yi ta yara wato Naira malala gashin tunkiya! Daga cikin wannan adadi na Dala biliyan dubu xaya, varayin shugabanni sun sace Dala biliyan 500, wato rabin kuxin sun voye su a qasashen waje yayin da kusan kashi 70 cikin 100 na ’yan Najeriya suke fama da qazamin talauci da quncin rayuwa da mayata da yunwa da cututtuka.

Waxannan varayin shugabanni sun kuma hana mutanen kirki zuwa kusa da mulki don kada a hana su ci gaba da sata da kisa ko a qwace abin da suka sata a hukunta su a tsawon shekara da shekaru.

Mafi sauqin halin da ake ciki a yanzu an samu shugaba ne da ake yi masa shaidar ba varawo ba ne, sai dai abin tambaya na kewaye da shi da sauran muqarrabai a tarayya da jihohi da qananan hukumomi da ma’aikatu da hukumomin gwamnati haka suke? Sanin kowa ne shugaban nan an kewaye shi da varayi suna hana waxanda ba ire-irensu ba su isa kusa da shi, balle su taimake shi wajen aiwatar da abin da ya kamata wajen gina qasa da hana ci gaba da sata da kisa da sauran laifuffukan da ake fama da su a qasar nan.

Ina fata Allah Ya karkato da hankalin zavavven Shugaban Qasa Alhaji Ahmed Bola Tinubu kuma Ya tunatar da shi tarihin Annabi Yusuf (AS) wanda ’yan uwansa suka jefa shi a cikin rijiya da ransa bisa fatar ya mutu ko wasu su tsince shi su tafi da shi wata qasa su sayar da shi, a qarshe sayarwar ta zama sanadin samun mulki gare shi. Allah Ya ganar da Tinubu ya gane makiran da za su jefa gwamnatinsa a hallaka su jawo masa baqin jini a idon jama’a don buqatunsu na samun qazamar dukiya. Ko waxanda za su haxa baki da maqiyansa don aikata abubuwan da zai yi yaqi da su.

Ya tuna yadda hatta a gwamnati da talakawa suka yi tsaye wajen kafuwar gwamnatin Shugaba Buhari da yadda aka riqa samun qorafe-qorafe cewa wasu sun kanainaye Buharin sun hana mutanen kirki da dama isa gare shi. Wanda hakan ya sa Uwargidan Shugaban Qasa Hajiya A’isha Buhari ta riqa kokawa a kafafen watsa labarai kan haka a shekarun baya. A wancan lokaci mutane da dama sun riqa suka da zarginta kan qorafin da ta yi, amma abin da mutane suka kasa ganewa shi ne ta fi kowa son mijinta ya samu nasara, ta fi kowa son ya yi abin kirki, ko ba komai ba, ta huta da gori da suka daga jama’a cewa mijinta ya gaza.

Abin takaici shi ne duk masu ilimin da muke da su na addini da na boko, sun kasa haxa kai su ilimantar da mu kan yadda za mu ceto qasar nan daga hannun miyagu tare da xora ta a kan hanyar ci gaba da kuma tabbatar da cewa masu mulki suna yin mulki na adalci kamar yadda Allah Yake so. Maimakon haka, sai suke taya vera vuruntu ta hanyar gwara kan mabiyansu, don a ba miyagun shugabannin damar ci gaba da aikata tu’annati da fasadi da varna da dukiyar jama’a. Wannan ya sa muka wayi gari yau kowace qabila ko kowane addini ko kowace jam’iyya ko kowace jiha, ba ta so a tava xanta da ya aikata ba daidai ba! Da wannan sai ya zamo ana siyasantar da komai a qasar nan ta yadda duk varnar da wani ya yi, sai a nuna ai don dalilin qabilarsa ko addininsa ko jam’iyyarsa ko yankinsa ake yi masa terere. Da wannan sai aka ci gaba da rasa kyakkyyawan shugabanci har ya zame jiki cewa duk lokacin da wani ya tafka varna to ya yi maza ya koma vangaren da ke mulki a jiha ko tarayya don samun mafakar da za a rufe wannan varna. Masu ilimin cikinmu duk suna ganin wannan hali, amma sun yi gum! Wasu daga cikinsu ma sun zama ’yan a bi yarima a sha kixa, da su ake shan lagwadar, wasu kuma sun zama masu raunin imani, sun kasa hanawa da hannu sun kasa faxa cewa abubuwan da ake yi ba daidai ba ne, yayin da wasu ma suke ganin ba laifi ba ne wanda aka ba shi amana ya kwasa ya riqa sammar da qalilan ga qalilan xin jama’a!

Masu hankali kuma suna gani ’ya’yansu suna ta aikata ta’asa da varna suna sata da fashi da makami da fashi da muqami da shaye-shayen miyagun qwayoyi suna fita daga cikin hankulansu suna aikata masha’a da zinace-zinace da luwaxi da maxigo da fyaxe da kisan kai, amma sun yi gum ko sun kawar da kawunansu daga haka! Saboda yanzu sun koma bautar ’ya’ya suna gudun vacin ransu! Kai wasu iyaye ma suna tafka sata ta fitar hankali ne saboda wai kada ’ya’yansu su shiga wahala a nan gaba,alhali su iyayensu sun haife su ne ba tare da su an tara musu dukiya ba.

Wani vangare da muka rasa mutanen kirki, shi ne yadda jami’an tsaro da alqalan da aka damqa musu amanar kamawa da hukunta masu aikata varna, kuma waxanda su da shugabannin Allah Ya xora musu alhakin kare rayuka da dukiya da addini da hankali da nasabar mutane amma sai ya zamo su ne suke lalata hankali da tsaro da shari’a domin su samu qazamar dukiya su ci karensu babu babbaka!

Don haka ina fata a yanzu da Cif Bola Tinubu ke shirin kama mulki, zai kafa wani kwamiti mai qarfin shari’a wanda zai qunshi mutane masu gaskiya da riqon amana su binciki kowa da komai; daga kan masu yin dokoki zuwa masu zartarwa da masu shari’a da shugabanni da ma’aikatan hukumomi da ma’aikatun gwamnati da su kansu hukumomin da suka haxa da Babban Bankin Najeriya (CBN) da Kamfanin Mai na Qasa (NNPC) da Fadar Shugaban Qasa da sauransu, a zazzage kowanensu a tabbatar da abin da kowa ya mallaka a lokaci da kafin gwamnatin Shugaba Buhari, kuxi da kadarori gida da waje. Duk wanda aka samu da dukiyar da ta fi qarfin samunsa a qwace kuma a hukunta shi don ya zame darasi ga na baya.

Gyaran qasar nan na buqatar yin amfani da abubuwan nan huxu da na ambata a sama, kuma babu wani daga waje da zai zo ya gyara mana, mu ne dai za mu tsaya mu yi aiki bilhaqqi da gaskiya mu gyara qasar nan.

Alhaji Abdulkarim Xaiyabu Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (MOJIN),

Tsohon Shugaban Qungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai da Ayyukan Gona ta Jihar Kano, (KACCIMA)

08060116666, 08023106666.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281822878047479

Media Trust Limited