dailytrust

Labarin Kura da Vera

Barkanmu da warhaka manyan gobe, tare da fatan ana lafiya. A yau na kawo muku labarin Kura da Vera. Labarin na qunshe da darussa da dama kamar na taimakawa xan uwa don ba a san abin da gobe zat a haifar ba.

Taku: Gwaggo Amina Abdullahi

Akwai wani zaki a wani daji da ake kira da suna ‘Dam’. Bayan zaki ya ci ya qoshi sai barci mai nauyi ya xauke shi a qarqashin wata bishiya. Can sai ga vera ya zo ya fara wasa a kan zaki. Zaki sai ya ji kamar ana wasa a kansa. Sai ya farka don ya ga abin da ya ta da shi daga barci. Can sai ya yi ido huxu da vera.

Vera sai ya razana ya gigice. Zaki ya ce sai ya kashe shi. Sai vera ya ba shi haquri. Kamar zaki zai kashe shi, can sai ya haqura ya bar shi.

Rannan vera ya zo wucewa sai ya ga zaki a kame a shingen maharbi. Sai vera ya je ya yanke shingen maharbi da haqoransa ya bar zaki ya fita. Tun daga nan sai suka zama abokanen juna.

To, Manyan Gobe, da zaki bai haqura ba a lokacin da vera ya ba shi haquri, da bai samu wanda zai cece shi ba, da maharbi ya kama shi. Da fatan manyan gobe za su zama masu taimako da haquri a duk inda suka tsinci kansu.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281827173014775

Media Trust Limited