dailytrust

Kwalliya Yadda za a tsaftace hammata

Daga Amina Abdullahi

Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan filin namu na kwalliya. A yau na kawo muku yadda ake kulawa da hammata. Idan an gyara jiki kada a manta cewa akwai inda ya fi muhimmanci da za a kula da shi. Musamman ma bayan an aske gashin wurin, akwai hanyoyi da za a bi don hana wajen yin baqi. Abubuwa da dama ne suke sa hammata ta yi baqi ko da an aske gashi. Yawan zufa da amfani da man cire gashin hammata da yawan qiba da kuma amfani da turare mai qarfi a hammata.

Amfani da man kwakwa: Babban abin da ake amfani da shi a wajen haxa man zamani shi ne man kwakwa domin yana xauke ne da sinadaran qara haske kuma yana da bitamin E. A shafa man kwakwa a hammata a kullum a yi minti goma kafin a yi wanka. Bayan an yi haka, sai a wanke da sabulu mara qarfi, wanda sinadaren da aka haxa shi ba masu zafi ba ne da ruwan xumi.

Amfani da gurji da lemon tsami: Kamar yadda aka san cewa ruwan lemon tsami na daxa hasken fata, haka kuma gurji shi ma na xauke da sinadarin qara wa fata haske da kuma sanya ta laushi da sulvi. A haxa ruwan lemn tsami da markaxaxxen gurji a wuri xaya sannan a shafa a hammata. A bari ya jima na tsawon mintuna goma sannan a wanke da ruwan xumi.

Garin kurkum da qwai: Kurkum ma na daxa wa fata haske. Za a iya kwava garin kurkum da ruwan qwai sannan a shafa a hammata bayan mintuna goma zuwa goma sha biyar sai a wanke da ruwan xumi. A kullum kafin a yi wanka.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281844352883959

Media Trust Limited