dailytrust

Yadda ake hax in qwai da nama

Daga Amina Abdullahi

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan filin namu na girkegirke. A yau na kawo muku yadda ake dahuwar qwai a cikin nama. Har ila yau ba zan fasa yi muku gargaxi a kan girki mai armashi wanda zai sanya maigida manta hularsa da kuma hana shi cin abinci a waje. Domin canza irin nau’ukan abinci a koyaushe shi ya sa na kawo muku wannan sabon salon girkin. A ci daxi lafiya. Abubuwan da ake buqata

· Qwai

· Ruwan qwai

· Fulawa

· Magi

· Garin busasshen burodi · Nama/ Sausage

· Kori

· Man gyaxa

Haxi

A tafasa qwai har sai ya nuna sannan sai a vare. Bayan haka, sai a samu ‘sausage’ a kwava shi da cokali. Bayan haka, sai a wanke hannu a goge. Sannan a zuba man gyaxa kaxan a tafin hannu a xora naman sannan sai a shafe shi a tafin hannun. A xauko dafaffan qwan sannan a lulluve shi. Bayan haka, sai a fasa kwai a zuba madarar ruwa kaxan ko nono a kwava. Sannan sai a tsoma qwan a ciki. Sai a samu fulawa a yaryaxa mata magi da kori a gauraya su sannan sai a saka kwan a ciki yadda fulawar za ta rufe qwan gaba xaya. Bayan haka, sai a sake tsoma kwan a ruwan kwan. A tsame sai a saka a cikin garin busashen biredi yadda garin biredin zai lulluve shi. A zuba man gyaxa a wuta bayan ya yi zafi, sai a soya. Sannan a tsame a sha da shayi.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281852942818551

Media Trust Limited