dailytrust

Saudiyya ta gayyaci Shugaban Iran zuwa qasarta

Qasar Iran ta ce Saudiyya ta gayyaci Shugaban Qasar Ebrahim Ra’isi domin zuwa wata ziyara a qasar, mako xaya bayan qasashen biyu sun amince su ci gaba da hulxar diflomasiyya.

An bayyana cewa batun gayyatar na qunshe ne cikin wata wasiqa da Sarki Salman na Saudiyya ya rubuta, sai dai mutanen qasar ba su tabbatar da hakan ba. Qasashen biyu da suke yankin Gabas ta Tsakiya, sun yi ta samun takun-tsaka na tsawon shekaru.

Qasar China na cikin qasashen da suka shiga tsakani wajen ganin qasashen sun koma ga xasawa da juna, abin da aka bayyana da cewa zai sauya siyasar yankin.

Wani babban jami’in gwamnatin Iran, Mohammad Jamshidi ya wallafa batun ziyara zuwa Saudiyyar a shafinsa na Twitter inda ya ce, Mista Ra’isi ya yi maraba da batun da kuma nanata cewa Iran na da zimmar faxaxa dangantaka.

Shi ma, Ministan Harkokin Wajen Iran, Hossein Amir-Abdollahian ya faxa wa manema labarai cewa, qasashen biyu sun amince su yi zama a matakin ministocin harkokin waje, inda ya ce an tsara gudanar da zaman ne a wurare uku. Sai dai bai bayyana sunayen wuraren ba, ko kuma sanar da ranar da za a yi zaman.

Kafar labarai ta BBC ya ruwaito cewa, wannan ci gaba da aka samu a dangantaka a tsakanin qasashen biyu a baya-bayan nan da China ta shiga tsakani na qara kyautata al’amura Qasashen sun sanar da cewa za su sake buxe ofisoshin jakadancinsu nan da wata biyu don sake qarfafa hulxar kasuwanci da kuma tsaro.

Qasashe da dama sun yi na’am da wannan ci gaba da aka samu, ciki har da Amurka da kuma Majalisar Xinkin Duniya, bayan yunqurin da aka sha yi na sulhunta qasashen a baya ya ci tura.

Saudiyya ta yanke dangantaka da Iran ne a 2016 bayan masu zanga-zanga sun afka wa ofishin jakadancinta a Tehran.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281930252229879

Media Trust Limited