dailytrust

Ku fito ku yi zanga-zanga don hana a kama ni — Trump

Tsohon Shugaban Amurka Mista Donald Trump ya kira ga magoya bayansa su fito su yi zanga-zanga don daqile yunquri da ya ce ana yi domin kama shi, duk da cewa babu wani bayani a hukumance game da iqirarin nasa da kuma tuhumar da ake yi masa.

Mista Donald Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social cewa yana ganin za a iya kama shi a kan laifin da ake zarginsa da aikatawa a birnin New York da ke da alaqa da biyan wasu kuxaxe ga wata tauraruwar ’yar wasan kwaikwayon nan Stormy Daniels.

Akwai zarge-zarge da dama a kan Trump da suka haxa da biyan kuxaxen yaqin neman zave ba bisa qa’ida ba da tsoma baki a yayin gudanar da zave da kuma yunqurin ganin an soke zaven Shugaban Qasa na 2020 bayan ya faxi a zaven. Haka ana tuhumarsa da kwashe manyan takardun sirri ya voye a gidansa bayan ya sauka daga karagar mulki.

A ranar Asabar da ta gabata ya bayyana cewa, “Ku gudanar da zangazanga don dawowa da qasarmu!”

Sai dai ba tare da wani tabbaci a hukumance ba, Trump, wanda yake neman sake tsayawa takarar a Jam’iyyar Republican a zaven Shugaban Qasa a baxi, ya wallafa wani saqo, yana cewa ana shirin kama “Jagora xan takarar Republican kuma tsohon Shugaban Amurka a ranar Talata (da ta gabata).”

Jami’an tsaro a birnin New York sun ci gaba da shirye-shiryen tabbatar da tsaro kan yiwuwar gurfanar da Trump a gaban kotu.

A cikin saqonnin nasa, Trump ya maimaita cewa zaven Shugaban Qasa na 2020 da ya sha kaye a hannun Joe Biden an “qwace masa ne” saboda zamba, kuma ya buqaci mabiyansa su yi zangazanga.

Bayan wannan iqirari da Trump ya yi na cewa shi ya samu nasara a zaven, ya nemi magoya bayansa masu tsattsauran ra’ayi su tayar da qayar baya a babban birnin qasar a ranar 6 ga Janairun 2021, sai dai a qarshe ya gaza gabatar da wata shaidar da za ta tabbatar da cewa shi ya yi nasara ba Biden ba.

Har ila yau a ranar Asabar, Trump ya aike da saqon imel ga magoya bayansa kan su tara kuxi, sannan ya sake buga wani saqo, inda ya yi kakkausar suka ga Gwamnatin Amurka da kuma yin kiran a gudanar da zanga-zanga.

Tsohon Shugaban na fuskantar zargin biyan wata tsohuwar ’yar fim xin batsa Stormy Daniels kuxi domin ta voye mu’amalar da suka yi ita.

Misis Daniels ta yi iqirarin cewa, Mista Trump ya yi hulxa da ita, kuma ta karvi Dala dubu130 daga hannun lauyansa kafin zaven 2016 domin kada ta tona alaqar da ke tsakaninsu.

Sai dai tsohon Shugaban ya musanta cewa ya yi lalata da Misis Daniels tun bayan zargin da aka yi masa a shekarar 2018.

“Mun yi lalata da Mista Trump a otal,” inji Misis Daniels, wadda ainihin sunanta shi ne Stephanie Clifford, lokacin da ta bayyana wa manema labarai a yayin wata gasar Golf a watan Yulin 2006.

Ta yi zargin cewa sun yi lalata sau

xaya a otal xinsa da ke gavar ruwan Tahoe, wani wurin shaqatawa a tsakanin Kalifoniya da 1HYDGD. Sai dai lauyan Mista Trump ya musanta zargin a lokacin.

“Da alama bai damu da lamarin ba. Ya kasance mai girman kai,” in ji Misis Daniels, yayin da take amsa tambayar da wata mai hira ta yi mata cewa ko Mista Trump ya ce ta yi shiru game da zargin yin lalatar.

Mai xakin Mista Trump, Melania Trump ba ta halarci gasar ba saboda ta haihu a lokacin.

‘Barazana da biyan kuxi domin in yi shiru’

A 2016 kwanaki kaxan kafin zaven Shugaban Amurka, Misis Daniels ta ce lauyan Trump, Mista Michael Cohen ya biya ta Dala dubu 130 domin ta yi shiru da bakinta kan alaqarsu da ita.

Ta ce, ta karvi kuxin ne saboda tana tsoron abin da zai faru da iyalanta idan ta qi karva.

Misis Daniels ta ce, an yi mata barazana iri-iri domin ta yi shiru.

A 2011, jim kaxan bayan ta amince ta tattauna da mujallar ‘In Touch’ kan zargin da take yi wa Trump ta ce, wani mutum da ba ta sani ba ya tunkaro ta da ’yarta a Las 9HJDV, inda ya faxa mata cewa ta “rabu da Trump.”

“Wannan yarinya kyakkyawa ce. Abin ba zai yi daxi ba idan wani abu ya samu mahaifiyarta,” in ji Daniels lokacin da take tuno abin da mutumin ya faxa mata, a wata tattaunawa da gidan talabijin ɗin CBS a 2018.

Ba a saka tattaunawar da ta yi da mujallar ba har sai a shekarar 2018.

Kafin a sa tattaunawar ta minti 60, Kamfanin Mai na Shell da ke da alaqa da Mista Cohen ya yi barazanar kai Misis Daniels kotu kan buqatar ta biya Dala miliyan 20, domin ta karya yarjejeniyar da suka qulla da ita.

Misis Daniels ta faxa wa CBS cewa, tana fuskantar barazanar biyan miliyoyin Dala idan ta yi magana a gidan talabijin, amma “abu mai muhimmanci ne a gare ni saboda in kare kaina”.

Shin sava qa’ida ne biyan kuxi don a voye laifin mutum?

Babu wani batun saɓa wa qa’ida idan wani ya biya kuɗi domin kada a bayyana abin da ya aikata.

Sai dai tunda an biya kuɗin ne wata ɗaya kafin gudanar da zaɓen Shugaban Qasar, masu sukar Mista Trump sun yi zargin cewa biyan kuɗin zai iya zama saɓa ka’idar yaqin neman zaɓe.

A watan Agustan 2018, Mista Cohen ya amsa laifin kauce wa biyan haraji da karya qa’idar kashe kuxaxe a yaqin neman zave da kuma biyan abokiyar Trump Misis Daniels kuxi.

Duk da cewa ya ce Mista Trump ba shi da alaqa da kuxin da aka biya, daga baya Mista Cohen ya ce, Mista Trump ne ya ba shi izinin biyan kuxin da suka kai Dala dubu130 domin a voye mu’amalarsa da matar, kwanaki qalilan kafin zaven 2016.

Shin za a iya kama Trump?

A qarshen mako Mista Trump ya ce ya yi imanin za a kama shi. Daga baya mai magana da yawunsa ya ce ba a sanar da su batun wata tuhuma da ake yi masa ba.

A farkon bana ne mai shigar da qara a birnin New York, Mista $OYLQ Bragg ya kafa wani kwamitin alqalai da zai binciki ko akwai isassun shaidun da za su iya sa a gurfanar da tsohon Shugaban Qasar kan kuxin da aka ba wa Misis Daniels.

Don haka shi ne wanda zai yanke hukunci ko za a yi tuhuma ko a’a, idan an gabatar da shi.

Wani kwamitin na gudanar da wani zama na sirri kuma mai gabatar da qara ya kafa shi ne domin tantance ko akwai isassun shaidun da za su iya sa a tuhumi Trump.

Idan aka gabatar da tuhumetuhumen su zama zargin laifi na farko da aka tava yi wa wani tsohon Shugaban Amurka.

A shafinsa na Truth Social, Mista Trump ya kira binciken da ake yi masa a matsayin bi-ta-da-qullin siyasa da tsarin shari’a da ke cike da cin hanci ke yi a kansa.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281934547197175

Media Trust Limited