dailytrust

Tsohon Shugaban Rasha ya nemi a harba makamai mai kan Kotun Duniya

Tsohon Shugaban Rasha Dmitry 0HGYHGHY ya nemi a kai harin makami mai linzami a birnin Hague idan Kotun Duniya ta kama Shugaban Qasar

3XWLQ.

0HGYHGHY wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Tsaro na Fadar Kremlin ya yi gargaxin cewa, “Haqiqa Kotun Duniya mai hukunta masu manyan laifuffuka za ta tafka babban kuskure idan har ta ba da umarnin a kama Shugaba Putin.”

Ya qara da cewa, kada a yi tunanin cewa ba za a iya yin amfani da wani makami mai linzami da za a harba daga wani jirgin ruwan yaqi na Rasha a Tekun Arewa ba zai faxa kan ginin kotun da ke Hague ba, don haka a bi a hankali.

0HGYHGHY ya kasance Shugaban Rasha ne daga 2008 da 2012, tsakanin wa’adin Putin na biyu da na uku, inda ya bayyana kotun da cewa ba ta da ikon kama Putin. Kotun dai ta ba da sammacin kama Putin ranar Juma’a, wanda shi ne karo na farko bayan kaurewar yaqin da take yi da Ukraine.

Jami’in na Kremlin ya yi kiran cewa, rugujewar kotun ta kusa, domin ba ta bin tsarin.

Gargadin ya zo ne yayin da Putin ya gana da Shugaban China, Xi Jinping a ranar Talata, inda Putin ya jinjina wa Shugaba Xi Jinping.

Kremlin ta ce shugabannin sun yi musayar ra’ayoyi a lokacin tattaunawarsu ta farko, kuma sun tattauna kan shirin zaman lafiyar qasar China da Ukraine, ba tare da yin wani qarin haske ba.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281943137131767

Media Trust Limited