dailytrust

Neman taimako lokacin da abubuwa suka yi tsanani

Barkanmu da sake haxuwa a wannan mako. Muna yi wa Ubangiji Allah godiya domin yawan alheranSa marasa misaltuwa a gare mu.

A wannan karo za mu yi nazari ne a kan inda za mu nemi taimako a lokacin da muke fuskantar tsanani.

“Zan ɗaga idanuna zuwa ga duwatsu; daga ina taimakona zai fito? Taimakona ya zo daga wurin Ubangiji, wanda Ya yi sama da ƙasa.” (Zabura 121:1-2)

Mai zabura yana tafiya zuwa Urushalima, kuma ya dubi duwatsun da suka kewaye ta. Koda yake yana nesa da cibiyar ibada, ya san Allah na kusa da shi. Taimakonsa ya fito daga wurin Ubangiji, wanda Ya yi sama da ƙasa.

Dukanmu muna buqatar mu xauke idanunmu daga matsalolinmu, mu xaga kanmu mu nemi Ubangiji, domin Shi kaxai ne mafita gare mu.

A ina kake/kike neman taimako? Ɗauki ɗan lokaci ka/ki yi tunani. Taimakonmu yakan fito ne daga wurin Ubangiji? Shin, Shi ne wanda muke fara juyawa gare shi lokacin buƙata? Mai Zabura ya dubi Ubangiji, wanda Ya yi sama da ƙasa, domin taimakonsa. Babu wani tushe mafi girma. Lokacin da kuka juyo zuwa ga Ubangiji, za ku samu kwanciyar hankali da ta wuce duk fahimta da farin ciki mara misaltuwa.

Ka ji, ya Ubangiji, sa’ar da na yi kuka da muryata. Kuma Ka yi mini rahama, Ka amsa mini. Sa’ar da Ka ce, “Ka nemi fuskata,” zuciyata ta ce maKa.

“Ya Ubangiji! Fuskarka zan nema.” Kada ka ɓoye fuskarKa daga gare ni. Kada Ka juyar da bawanKa da fushi;

Kai ne taimakona; Kada Ka yashe ni, kuma kada Ka yashe ni. Ya Allah na ceto! Domin mahaifina da mahaifiyata sun rabu da ni. Amma Ubangiji zai ɗauke ni. Ka koya mini hanyarKa, ya Ubangiji, Kuma Ka shiryar da ni ga hanya madaidaiciya Saboda maqiyana. Kada Ka bashe ni ga burin abokan gabana, Gama shaidun ƙarya sun taso a kaina.

Kuma kamar shaqar tashin hankali. (Zabura 27:7-12)

Maimakon mu binciki waɗannan ayoyi ɗaya bayan ɗaya, bari mu duba su gaba ɗaya. Ina son mu waiwaya baya mu lura da muhimman umarni na musamman a cikin waxannan ayoyi.

Aya ta 7: “Ka ji . . . Ka yi alheri . . . Ka amsa mini!”

Aya ta 9: “Kada ka ɓoye fuskarKa . . . “Kada Ka yashe ni!”

Aya ta 11: “Ka koya mani . . . Ka ba ni!”

Aya ta 12: “Kada Ka bashe ni ga magabtana!

Dauda bai roƙi wani abin da Allah bai riga ya yi alqawari ba. Zai yi kyau mu yi koyi da marubucin Zabura ta wajen yin irin wannan addu’a a yau. Haqiqa Ubangiji Ya riga Ya so Ya cika waɗannan buƙatu. Saurari wasu ayoyi guda uku a kan wannan batu.

Don haka bari mu matso da gabagaɗi zuwa ga Kursiyin Alheri, domin mu samu jin ƙai, mu samu alherin taimako a lokacin buqata. (Ibraniyawa 4:16).

Addu’ar mai adalci tana iya cika abubuwa da yawa. (Yakubu 5:16)

Kada ku damu da kome, amma a cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya ku bar roƙeroƙenku su sanu ga Allah. (Filibbiyawa 4:6)

Dauda ya fuskanci yanayi mai wuya. Ya sha wahala da yawa kuma yana buqatar taimako. Miyagun mutane sun tasar masa don su cinye namansa. Maƙiyan sun kai masa hari kuma sojoji masu ƙarfi sun kewaye shi. Yaƙi ya tashi a kansa. Ya fuskanci zargin shaidun ƙarya.

Yana cikin waxannan matsaloli, ya yi kira ga Allah. Da yake jin rauni da kaxuwa, sai ya qasqantar da kansa, ya roki Allah ya ji muryarsa. Ya san cewa babu wanda zai iya taimakonsa, amma idan ya nemi fuskar Allah, zai ji shi, Ya ji tausayinsa, kuma Ya amsa masa.

Da ya waiwaya baya, ya tuna cewa Allah Ya kasance da aminci a koyaushe kuma Ya cece shi daga kowane tsoro. Maharansa sun yi tuntuɓe sun faɗi. Ya kasance lafiya a gabansa, har ma an “ɗauka bisa maƙiyan da suka kewaye ni.” Ya dogara ga Allah, zuciyarsa cike da farin ciki, kuma ya iya rera waƙoƙin yabo.

Wannan tunasarwa ce mai ƙarfi sa’ar da muke jin matsaloli sun kewaye mu. Muna iya jin cewa buqatun kuɗi sun shafe mu, za a iya samun savani a cikin dangantakarmu. Wataƙila muna da matsalolin lafiya ko kuma mu fuskanci matsi a kan aiki. Wataƙila mu damu da abokai da dangi. Ko kuma muna iya yin kokawa ta ruhaniya. Littafi Mai tsarki ya yi alqawari cewa, a duk wannan yanayi, ba ma buqatar mu ji tsoro ko damuwa. Maimakon haka, waɗannan lokata ne na neman fuskar Ubangiji Allah. Kada a yi gajerun addu’o’i na ladabi amma ta zahiri ta wurin neman fuskar Ubangiji, mu kuma kusance shi gaba-gaɗi, tare da raɗaɗi da gaggawa.

A yau, nemi fuskar Allah a cikin rayuwarmu don matsalolin da muke fuskanta.

Bari Ubangiji Allah Ya bishe mu, amin.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281947432099063

Media Trust Limited