dailytrust

Azumi na gaskiya

Daga Huxubar Sheikh Abdulbari bin Iwad As-Sabitiy

Masallacin Annabi (S.A.W), Madina Fassarar Salihu Maqera

Huxuba ta Farko

Godiya da hamdala ga Allah.

Bayan haka, ku bi Allah da taqawa a kan haqqin binSa da taqawa, domin Allah Maxaukaki Ya ce: “Ya ku waxanda suka yi imani! Ku bi Allah da taqawa a kan haqqin binSa, kuma kada ku mutu face kuna masu sallamawa (Musulmi)” (Q:3:102).

Ranaku suna shuxewa kamar shuxewar girgije, shekaru suna wucewa da sauri, alhali muna cikin mayen RAyuwa muna shagaltattu. ’Yan kaxan ne suke tunani kan halin da muke ciki ko makomarmu. Allah Maxaukaki Ya ce: “Kuma Shi ne Wanda Ya sanya dare da wuni a kan mayewa, ga wanda yake son ya yi tunani, ko kuwa ya yi nufin ya gode.” (Q:25:62).

Musulmi a cikin shekarunsa abin iyakancewa ne, kuma rayuwarsa gajera ce. Allah Ya sanya masa wasu ayyukan musamman na alheri, kuma Ya ba shi daga zamani da wuri masu daraja da za su kange shi daga karkacewa su daidaita rayuwarsa. Daga cikin waxannan ayyuka akwai azumin watan Ramadan Mai albarka. Allah Maxaukaki Ya ce: “Ya ku waxanda suka yi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waxanda suke gabaninku, tsammaninku za ku yi taqawa.” (Q:2:183).

A cikin watan Ramadan takun sha’awoyi kan ragu a zukata masu imani. Ayyukan qanqan da kai su xaukaka a cikin wuni da dare. Wani yana roqon afuwa a kan gazawarsa, wani yana roqon dacewa a cikin ayyukan xa’arsa, wani yana isti’aza daga uquba, wani yana fatar kyakkyawan lada, wani kuma zikiri ya shagaltar da shi daga roqonSa. Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya datar da su, yayin da aka haramta hakan ga wasunsu.

Watan Ramadan wata ne na qarfi da kyauta, wata ne na raya dare da imani, wata ne na aiki da haquri. Ba wata ne na rauni da kasala da barci ba. Kasalar wasu masu azumi da komawarsu ga barci a wuninsa da qaranta ayyukan xa’a sun sava wa hikimar yin azumi, ba su dace da manufarsa ba.

Musulmin farko sun kasance suna rayuwa ne a cikin Ramadan da zukatansu da hankalinsu, idan xayansu na azumi, haqiqa yana kiyaye wuninsa yana mai haquri kan wahalhalu, yana kiyaye dokokin Allah da jin tsoronSa. Mai yin nesa da duk abin da zai vata azuminsa. Ba ya furta mummunar magana, ba ya faxin komai sai alheri, ko ya yi shiru. Kuma darensa ya kasance yana kashe shi ne cikin Sallah da tilawar Alqur’ani da zikiri domin koyi da Manzon Allah (S.A.W).

Ribar azumi da sakamako da falalarsa ba su da iyaka, qidaya ba ta qididdige su. Sai dai masu kasala ba su samu, masu wasa da suke vata watan a barci, ko kai dare a shagunan kasuwanci da kashe dare ana wasa da shagala.

Azumi garkuwa ne daga wuta kamar yadda Ahmad ya ruwaito daga Jabir (RA) cewa: “Lallai Annabi (S.A.W) ya ce: “Abin sani azumi garkuwa ne da ke kange bawa daga wuta.” Azumi garkuwa ne daga sha’awoyi, domin haqiqa ya zo a cikin Hadisin Ibn Mas’ud (RA) cewa: “Lallai Annabi (S.A.W) ya ce: “Ya ku taron samari! Wanda yake da ikon yin aure daga cikinku, to ya yi aure, domin shi ya fi runtsewa ga ido da kuma kange farji. Wanda kuma ba ya da iko, na hore shi da yin azumi, domin shi garkuwa ne gare shi.” Buhari da Muslim suka ruwaito.

Azumi hanya ce ta zuwa Aljanna, Nisa’i ya ruwaito daga Abu Amama ya ce: “Na zo ga Manzon Allah (S.A.W) na ce: “Ka umarce ni da wani al’amari da zan riqe daga gare ka.” Sai ya ce: “Na hore ka da yin azumi, domin babu kamarsa.”

An karvo daga Sahlu bin Sa’ad (RA) cewa: “Lallai Annabi (S.A.W) ya ce: “Lallai a cikin Aljanna akwai wata qofa ana ce da ita: Rayyan. Masu azumi ne za su shiga ta cikinta a Ranar

Qiyama, babu mai shiga ta cikinta bayan su. Za a riqa cewa ina masu azumi? Sai su tashi, babu mai shiga ta cikinta sai su. Idan suka shiga sai a kulle, babu mai shiga a bayansu.” Buhari da Muslim suka ruwaito.

Haqiqa Imam Ahmad ya ruwaito daga Abdullahi bin Amru bin Al-As (RA) cewa: “Lallai Annabi (S.A.W) ya ce: “Azumi da Alqur’ani suna ceton bawa a Ranar Qiyama. Azumi zai ce: “Ya Ubangiji! Na hana shi abinci da sha’awoyi da rana, Ka ba ni cetonsa. Alqur’ani kuma ya ce: “Na hana shi barci cikin dare, Ka ba ni cetonsa. Ya ce: “Sai su yi ceto su biyun.”

Azumi kaffara ce da gafara ga zunubai, domin kyawawan ayyuka suna kankare munana. Haqiqa (S.A.W) ya ce a Hadisin Abu Huraira (RA): “Wanda ya yi azumi yana mai imani da neman lada, an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa.”

Azumi sababi ne na samun sa’ada a duniya da Lahira. Manzon Allah (S.A.W) ya faxi a Hadisin Abu Huraira cewa: “Na rantse da wanda ran Annabi Muhammad ke hannunSa, warin bakin mai azumi ya fi soyuwa a wurin Allah daga qanshin turaren almiski. Kuma mai azumi yana da farin ciki biyu: idan ya yi buxa-baki da kuma in ya haxu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da azuminsa.” Buhari da Muslim suka ruwaito.

Shin za mu sanya wa Ramadan wani lokaci ya zama na komawa ga Allah da hisabi ga kawunanmu da kyautata inda muka gaza a vangaren Allah? Shin ko xaliban ilimi da masu da’awa za su sanya Ramadan ya zama wani lokaci na jaddada himma da tsarkake niyya? Ko kuwa Ramadan zai kasance wata fursa ce da kowane Musulmi zai taimaki xan uwansa azzalumi ko wanda ake zalunta? Ya taimaki wanda ake zalunta ta hanyar qwato masa abin da aka zalunce shi, ya taimaki azzalumi ta hana shi yin zaluncin, sai mutanen kirki su shugabanci al’ummar Musulmi. Ko kuwa Ramadan zai kasance wata fursa ga mawadata su biya buqatun faqirai, su yi shukura kan ni’imar da aka yi musu ta hanyar ajiye ta a inda Wanda Ya ba su ni’imar Ya ce, ta yadda za su iya ceto mayunwata daga al’ummar Musulmi? Imaninsu yana iya faxawa ga haxari, idan suka gaza ciyar da mayunwatansu ko tufatar da marasa tufafinsu ko shayar da masu jin qishinsu. Ko kuwa Ramadan zai kasance wani lokaci da kowane Musulmi zai fahimci kasala da rashin kazar-kazar na iya jefa shi ga aikata kaba’ira, ta yadda zai ciru daga aikata giba da annamimanci da mugun zato da tozarta wasu da raina xan uwansa Musulmi?

Ya ku bayin Allah! Ramadan babbar makaranta ce da muke samun horo a dare da ranarsa, gavvanmu suke qarfafa da shifttarsa har sai sun yi kamar yadda Ubangiji Mahaliccinsu Ya yi nufi. Ya zo a cikin Hadisin Qudusi cewa: “BawaNa ba zai gushe yana kusantaTa da nafilfili ba, har sai Na so shi. Idan Na so shi, sai in kasance jinsa da yake ji da shi da ganinsa da yake gani da shi da hannunsa da yake damqa da shi da qafarsa da yake tafiya da ita.” Buhari ya ruwaito.

Makarantar azumi tana tarbiyyantarwa kan qarfi da gaskiyar niyya. Waxannan su ne ke karya turakun son zuciya su mayar da igiyoyin sharri. Za a ga mumini yana riqe da akalar rayuwarsa yana hana ta faxawa ga sha’awoyi ko abubuwan son zuciya. Kai yana iya ce wa zuciyarsa na qi. Me ya fi daxi a ce ta kasance cikin neman yardar Allah. Ba ta jima’i da rana ba ta fasiqanci. Kuma da jahili zai vata mata ya nemi tayar da hankalinta, sai ya yi mata linzami daga fisgar sharri ta faxin: “Ni mai azumi ne!”

Azumi na gaskiya yana tsarkake zuciya daga miyagun qulle-qulle da zunubai da sharri. Yana kange harsuna daga furta maganganun banza da hana ido ganin haram.

Amma daga cikin masu azumi akwai mai azumin da ba ya da komai sai yunwa da qishin ruwa. Domin mutumin da ke barin abinci, amma ya ci naman ’yan uwansa da giba, yana kamewa daga abin sha, amma bai kamewa daga qarya da algushu da zaluntar mutane, yunwa da qishi kawai yake sha.

Azumi na gaskiya yana sa Musulmi ya zama mai faffaxar zuciya da harshe mai laushi, ya zamo mafi gudu daga husuma da sharri, idan aka yi masa laifi ko aka munanan masa ya yi haquri. “Masu haquri kawai ake cika wa ijararsu, ba da wani lissafi ba.” (Q:39:10).

Daga cikin albarkar wannan wata mai girma, akwai tsayuwar dare, haqiqa Manzon Allah (S.A.W) ya kwaxaitar kan Tsayuwar Ramadan yana cewa: “Wanda ya yi Tsayuwar Ramadan yana mai imani da neman lada an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa.” Sai yin kyauta da sadaka, saboda Annabi (S.A.W) ya fi dukkan mutane yin kyauta, kuma ya fi yin kyauta da sadaka a cikin Ramadan lokacin da yake ganawa da Jibrilu kamar yadda Buhari da Muslim suka ruwaito. Kuma an so a gaggauta buxa-baki da yin addu’a yayin shan ruwa. Haqiqa Tirmizi ya ruwaito cewa: “Lallai Annabi (S.A.W) ya ce: “Mutum uku ba a mayar musu da addu’arsu: Shugaba adali da mai azumi lokacin da yake buxabaki da kuma wanda aka zalunta.”

Ya bayin Allah! Ku yi salati ga Manzon shiriya. Haqiqa Allah Ya umarce ku da hakan a cikin LittafinSa: “Lallai Allah da Mala’ikunSa suna salati ga Annabi. Ya ku waxanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, ku yi sallama domin amintarwa a gare shi.” Ya Ubangiji! Ka qara tsira da aminci a bisa bawanKa, kuma ManzonKa Muhammad da alayensa da sahabbansa.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281951727066359

Media Trust Limited